Kotu Ta Tura Shugaban EFCC, Bawa, Kurkukun Kuje, Ta Umurci IGP Da Ya Kama Shi
- Babbar kotun jihar Kogi ta umurci Sufeto Janar nay an sanda da ya kamo mata tare da garkame shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa, a kurkukun Kuje na tsawon kwanaki 14
- An tattaro cewa Bawa ya ki bin umurnin da kotu ta bayar a baya a shari’ar wani Ali Bello
- Bello ya shigar da karar shugaban na EFCC a kotu kan ikirarin cewa ya kama shi tare da tsare shi ba bisa doka ba
Kogi - Kotu ta yi umurnin garkame shugaban hukumar yaki da cin hanci da hana yi wa tattalin arziki zagon kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, a gidan gyara hali na Kuje kan kin bin umurninta.
Jaridar Daily Independent ta rahoto cewa, an umurci Sufeto Janar na Yan Sanda da ya tabbatar da kama Bawa tare da tsare shi a gidan yari nan da kwanaki 14 masu zuwa har sai ya wanke kansa daga zargin da kotu ke yi masa.
Dalilin da yasa kotu ta hukunta shugaban EFCC, Bawa
Da yake yanke hukunci a ranar Litinin, 6 ga watan Fabrairu, Justis R.O. Ayoola na babbar kotun jihar Kogi ya amince da bukatar da aka nema na garkame shugaban na EFCC saboda kin bin umurnin kotu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
An tattaro cewa Bawa ya saba umurnin da kotu ta bayar a watan Nuwamban 2022 lokacin da ta nemi ya aiwatar da bukatunta a shari'ar Ali Bello.
Ali Bello ya maka Bawa a kotu kan kama shi da tsare shi ba bisa ka'ida ba, inda ya yi nasara kotu.
Sai dai kuma bayan nan EFCC ta gurfanar da shi kan zargin wawure kudi kwanaki uku bayan zartar da wancan hukunci.
Kotu ta yi watsi da bukatar hukumar yaki da cin hanci da rashawar na neman a jingine wancan hukuncin bisa hujjar cewa bai da inganci, rahoton The Sun.
Daily Trust ta kuma rahoto cewa kotu ta umurci wadanda ake kara da su rubuta wasikar ban hakuri kan shari'ar a jaridar kasar sannan su ba mai karar naira miliyan 10 a matsayin diyya.
Kotu Ta jingine ukuncin kama Shugaban Hukumar EFCC kan saba umurninta
A gefe guda, mun kawo a baya cewa babbar kotun Abuja ta ajiye shari'ar da umurnin da aka bada na daure shugaban hukumar yaki da rashawa, EFCC, Abdulrasheed Bawa, kan saba umurnin kotu.
Asali: Legit.ng