Sauya Naira: Emefiele Na Kokarin Haddasa Rudani a Zabe Ne, Inji Ganduje

Sauya Naira: Emefiele Na Kokarin Haddasa Rudani a Zabe Ne, Inji Ganduje

  • Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya zargi gwamnan CBN, Godwin Emefiele, da kokarin haddasa rudani a zaben 2023
  • Ganduje ya ce Emefiele ya sauya kudin Najeriya a daidai wannan lokaci ne saboda haushin bai samu tikitin takarar shugaban kasa a APC ba
  • Yayin da take bayyana cewa bata goyon bayan sauya kudi a yanzu, gwamnatin Kano ta ce za ta rabawa mutane kayan rage radadi a fadin kananan hukumomi 44

Kano - Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya yi ikirarin cewa da gangan gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya aiwatar da manufar sauya kudi cikin dan kankanin lokaci.

Ganduje ya ce Emefiele ya yi hakan ne saboda haushin gaza samun tikitin takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressive Congress (APC).

Emefiele da Ganduje
Sauya Naira: Emefiele Na Kokarin Haddasa Rudani a Zabe Ne, Inji Ganduje Hoto: Within Nigeria
Asali: UGC

Ya bayyana hakan ne a wajen yakin neman zaben jam'iyyar wanda ya gudana a Tsanyawa a ranar Lahadi, 5 ga watan Fabrairu, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Rikici Ya Barke a APC na Taraba, An Fitittiki Shugaban Jam'iyya

A wajen gangamin kamfen din ne gwamnan na Kano ya gabatar da dan takarar gwamnan APC, mataimakinsa da sanatocin jam'iyyar da sauransu ga mutanen jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar wata sanarwa da sakataren labaran gwamnan, Abba Anwar, ya saki, Ganduje ya ce:

"Gwamnan na CBN na aikata hakan ne kawai don haddasa rudani a zabe mai zuwa saboda wasu dalilai marasa tushe.
"Tsawon lokaci yanzu, gwamnan na CBN yana cikin bakin ciki saboda gaza samun tikitin takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyarmu mai albarka ta APC."

Gwamnatin Kano bata tare da Emefiele, Ganduje

Gwamna Ganduje ya fito karara ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kano da jam'iyyar APC a jihar basa tare da wannan mataki na gwamnan CBN, rahoton Daily Post.

Ya ci gaba da cewa:

"Sauya kudi abu ne da ake yi a fadin duniya, amma ba yadda muke fuskanta a kasarmu ba. Lokacin bai dace ba, wa'adin da aka bayar baya bisa daidai kuma da gangan aka yi haka."

Kara karanta wannan

2023: Hadimin Gwamna Mai Ci Ya Sauya Sheka Daga PDP Zuwa APC a Wata Jihar Arewa

Gwamnan na Kano ya jero wasu matakai da za su dauka don saukaka mawuyacin halin da sauya kudin ya jefa mutane a ciki kaar haka:

"Za mu sammaci manajojin bankiu nan ba da jimawa ba don yi masu tambayoyi kan karancin sabbin kudi a bankuna.
"Ya kamata su zo nan sannan su yi mana bayani, menene dalilin da yasa mutanenmu ke shan wahala kan wannan lamari na sauya naira. Zan ziyarce su da kaina don sanya ido kan abun da ke faruwa da dalili."

Gwamnatin Kano za ta raba kayan rage radadi a fadin kananan hukumomi 44

Ganduje ya bayyana cewa a lokacin annobar korona, gwamnatin jihar ta raba kayan rage radadi ga al'umma a fadin kananan hukumomi 44.

Ya ce:

"Muna shirin fara raba kayan rage radadi nan ba da jimawa a fadin kananan hukumomi 44, don rage radadin wannan mawuyacin hali da gwamnan CBN ya haddasawa mutanenmu."

Gwamnatocin Kaduna, Kogi da Zamfara sun maka Buhari da CBN a kotu

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Budewa Tsohon Ministan Buhari Wuta, Mutum Biyu Sun Mutu

A wani labarin kuma, mun ji cewa gwamnatocin arewa uku sun damu da mawuyacin halin da al'ummar kasar ke ciki inda suka maka gwamnatin tarayya da babban bankin Najeriya a kotun koli.

Jihohin Kaduna, Zamfara da Kogi sun bukaci kotun ta hana gwamnatin tarayya aiwatar da wa'adin da ta bayar da daina amfani da tsoffin kudi a kasar

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng