Kuyi Hakuri Da Wahalar Karancin Naira Kamar Yadda Kuke Hakuri Da Shan Magani Idan Baku Da Lafiya:Ministar Kudi
- Hajiya Zainab Shamsuna ta yi maganarta ta biyu kan lamarin sauya fasalin takardun Naira
- Ministar da farko ta bayyana cewa ita bata fahimci alakar inganta tattalin arziki da sauya fasalin kudi ba
- Yanzu kuma ta ce sauya fasalin kudin na da amfani kuma yan Najeriya sun rungumi kaddara
Abuja - Ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed Shamsuna, ta yi kira da yan Najeriya su yi hakuri da wahalhalin da suke sha game da karancin kudi sakamakon sauya fasalin manyan takardun Naira.
Ministar ta bayyana hakan yayin hira da manema labarai a fadar shugaban kasa ranar Alhamis, rahoton TheCable.
Zainab ta ce wahalar za ta zo ta kare amma abinda gwamnatin ke yi shine daidai don gyara tattalin arzikin Najeriya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sauya Naira: Manyan Arewa Sun Fada Wa Shugaba Buhari Abinda Zai Faru Idan Ya Ki Bin Umarnin Kotun Koli
Tace:
"Ba mu jin dadin yadda mutane ke layi da gwagwarmaya a ATM don samun kudi. Amma abune mai karewa."
"Bari in baku misali. Idan kana fama da ciwo, wajibi ne a zuba magani idan kana son ya warke."
"Wani lokacin kuma idan kaje asibiti, za'a zuba maka iodine kuma da zafi. Amma abune da kake bukata don ka warke."
Ministar ta kara da cewa sauya fasalin Nairan zai taimawa wajen yaki da rashawa.
Tsadar Mai Da Naira: A Tausayawa Talaka: Gwamnan Balaga Gwamnatin Tarayya
A wani labarin daban, Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammad Abdulkadir, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta dubi Allah sannan ta duba halin da talakawa suka shiga sakamakon sauya fasalin Naira.
Gwamnan wanda aka fi sani da Kauran Bauchi ya ce mutane basu tsira da wahala da tsadar man fetur ba, gashi yanzu ko kudin sayan man babu.
Kaura ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar shafinsa na Facebook ranar Alhamis, 2 ga watan Febrairu, 2023.
A cewarsa:
"Baya ga wahalar ƙaranci da tsadar man fetur, kalanzir da iskar gas da aka shafe fiye da shekara a ciki musamman a nan Arewa, al'uma na cikin matsanancin ƙunci sakamakon canjin kuɗi.
A mafi yawancin wurare babu tsoffin kuɗaɗen balle sabo, kafin a same su kuma sai an sha baƙar azaba.
Asali: Legit.ng