Tsohon Sarkin Kano Na Son Kasheni, Gwamnan jihar Benue Ya Koka

Tsohon Sarkin Kano Na Son Kasheni, Gwamnan jihar Benue Ya Koka

  • Kuma dai, gwamna Benue ya ce wasu yan kabilar Fulani na shirya hallakashi kan abinda bai da alhaki
  • Ortom yace Sanusi Lamido Sanusi tare da wasu jiga-jigan Fulani sun kai kararsa wajen Buhari
  • Bidiyo ya nuna tsohon sarki Sanusi yana alhinin kisan gillan da aka yiwa Fulani a garin Doma

Makurdi - Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bayyana cewa rayuwarsa na cikin mumunan hadari saboda tsohon Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi, na ingiza wata kungiyar su hallakashi.

Ortom, ya bayyana hakan a hira da manema labarai na musamman da yayi a gidan gwamnatin jiar ranar Alhamis, rahoton Sun.

Ya ce wasu jagororin Fulani 52 karkashin jagorancin Sanusi Lamido Sanusi sun kai kararsa wajen shugaba Muhammadu Buhari cewa shi ke da alhakin kashe Fulani kimanin 40 da Bam a karamar hukumar Doma a jihar Nasarawa.

Kara karanta wannan

Daga Bisani, Khalifa Sanusi II ya Fallasa Irin Kiyayyar da Ortom ke wa Fulani, Ya Fada Daga Inda aka Shirya Halaka Makiyayan Nasarawa

Sanusi
Tsohon Sarkin Kano Na Son Kasheni, Gwamnan jihar Benue Ya Koka Hoto: Sun
Asali: Facebook

Gwamnan ya ce wata kungiya na daura alhakin kisan Fulani da hukumar gandun dajin jihar Benue kuma su suka sanar da Sojoji cewa su jefa musu Bam.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa:

"Wata kungiya na tuhumata da kashe makiyaya. Tsigaggen Sarki Sanusi bayan haka ya yi bidiyo a Hausa inda ya soke ni kuma yayi kira ga dukkan Fulani su dauke ni makiyi kuma al'ummar Benue kada su zabeni a zabe mai zuwa."
"Gaskiya wadannan tuhume-tuhume da ake yimin da gwamnatin Benue wani sabon shiri ne na makiya jihar nan su kashe ni."
"Jawabin wannan kungiya karkashin Lamido Sanusi rainin hankali ne ga dubban mutan Benue da Fulani Makiyaya suka kashe."

Ya kara da cewa zai aike wasikar kar-ta-kawana ga Shugaban kasa inda zai bukaci a gaggauta damke Lamido Sanusi kan shirin kasheshi.

Buhari ya yi abin kunya, har yanzu bai yi magana kan kisan Fulani da Bam a Nasarawa: Miyetti Allah

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan Bindiga Sun Budewa Dan Takaran Gwamnan Jihar Ebonyi Wuta, An Kashe Direbansa

Kungiyar kare hakkin makiyaya ta Miyetti Allah MACBAN ta bayyana takaicinta game da shirun gwamnatin tarayya da Shugaba Muhammadu Buhari kan harin Bam din da ya hallaka Fulani Makiyaya 40 a jihar Nasarawa.

Kakakin kungiyar Miyetti Allah, Muhammad Abdullahi, ya bayyana cewa wannan kisan gilla aka yiwa al'ummarsu kuma wajibi a gudanar da bincike kan yadda Bam ya tashi da su,

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida