Fasto Ya Yada Labarin Karya Cewa Ya Mutu Gudun Kada Ya Biya Bashin N3m
- Hukumar ta cika hannu da wani faston coci wanda yayi kokarin yaudarar wani mabiyinsa
- Lokaci bayan lokaci labarai na fitowa kan yadda masu ikirarin malamta ke aikata abin kunya
- Alkalin kotu ta bada belinsa kuma ta bukaci akalla mutum biyu da zasu tsaya masa don kada ya gudu
Ondo - Ana tuhumar wani faston Coci a jihar Ondo, Paul Oyewole, da laifin yada labarin mutuwar kansa a manhajar WhatsApp gudun kada ya biya bashin ₦3 million da wani mabiyinsa ke binsa.
An gurfanar da Fasto ne a kotun majistaren birnin Ondo.
Vanguard a ranar Laraba ta ruwaito cewa Fasto Oyewole ya karbi bashin ₦3 million hannun wani mamban cocinsa, Boyede Emmanuel, kuma yayi alkawarin biya cikin kwanaki bakwai, amma bai cika ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
2023: A Karshe Atiku Ya Magantu A Kan Fallasar Da Tsohon Hadiminsa Ya Yi Masa Kan Zargin Wawure Kudi
Lauyan hukumar, Akao Moremi, ya sanar da Alkalain kotun cewa bayan gaza cika alkawarin, Faston sai ya wallafa labari a manhajar WhatsApp cewa ya mutu bayan tura sakon bankin karya cewa ya biya bashin.
Yace:
"Ya yiwa wanda ya shigar da shi kara waya ind ayake masa barazanar cewa zai yi tsindir a kofar gidansa."
"Ya aikata laifin tsakanin ranar 25 ga Nuwamba, 201 da kuma ranar 7 ga Mayu, 2022, a unguwar Valentino na jihar Ondo."
Faston ya karyata zargin da ake masa kuma an bada belinsa kan ₦1 million, riwayar Herald.
Alkalin kotun, Mosunmola Ikujuni =, ta dage zaman zuwa ranar 13 ga Febrairu, 2023 don cigaba don sauraron karar.
Ko Mai Lita 20 Nake Zubawa Janareto: Bidiyon Fasto Yana Balbale 'Yan Coci da fada Kan Bada Sadakar N100 da N20
A wani labarin kuwa mai kama da wannan, Wani fasto ya caccaki mabiyansa bisa irin kananan kudaden da suke sayanwa a asusun sadakar coci idan lokacin bada kudi yayi.
Faston ya tsinewa masu sanya N100 cikin akwatin sadaka inda yace ko kudin man janareton da ake amfani da shi a cocin ba karamin kudi bane.
Yan Najeriya da dama sun tofa albarkatun bakinsa kan wannan bidiyo da ya yadi a kafafen ra'ayi da sada zumunta.
Yayinda wasu suka goyi bayan faston suka ce gaskiya yake fasa, wasu sun ce ibada ba sai da kudi ake yinsa ba.
Asali: Legit.ng