Hadimar Gwamna Tambuwal, Aishat Maina, Ta Mutu Sakamakon Cinkoso Lokacin Kamfen Atiku a Sokoto

Hadimar Gwamna Tambuwal, Aishat Maina, Ta Mutu Sakamakon Cinkoso Lokacin Kamfen Atiku a Sokoto

  • Daya daga cikin na kusa da gwamna Aminu Waziri Tambuwal ta mutu sakamakon cinkoso lokacin kamfe
  • Dubunnan mutane sun halarci taron kamfen Atiku/Okowa yau a Sokoto kuma Legit ta kawo muku bayanai kai tsaye
  • Abokan aikinta sun yaba halayen marigayiyar kuma sun yi addu'an Allah ya gafarta mata kura-kurenta

Sokoto - Babbar mai baiwa gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, shawara kan ilimin mata, Hajiya Aisha Maina, ta rigamu gidan gaskiya.

Hajiya Aisha Maina ta mutu ne yan mintuna bayan halartan taron kamfen dan takarar shugaban kasa jam'iyyar PDP da ya gudana a jihar, rahoton Daily Trust.

An tattaro cewa Hajiya Maina ta shiga cikin wani cinkoso da hargitsi da ya uku a hanyar fita daga cikin filin kwallon Giginya, inda taron ya gudana.

Wata majiya a ma'aikatar labaran jihar wacce ta bukaci a sakaye sunanta tace:

Kara karanta wannan

Hisbah ta kammala bincike kan labarin matar da ta auri saurayin diyarta a Kano, Ga sakamako

"Wata mai babur ya fadi daga kan babur dinsa yayin da yake kokarin fita daga filin kwallon kuma hakan ya tada hargitsi, mutane suka fara fadawa kan juna. Tana daya daga cikin wanda ta ritsa da su."
Hajia
Hadimar Gwamna Tambuwal, Aishat Maina, Ta Mutu Sakamakon Cinkoso Lokacin Kamfen Atiku a Sokoto Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugaban kwamitin masu baiwa gwamnan shawara, Magaji Gusua shi ma ya tabbatar da aukuwan lamarin inda yace da wuri aka garzaya da ita asibitin koyarwa jami'ar Usmanu Danfodiyo.

A cewarsa:

"Amma abin takaici yan mintuna da kwantar da ita ta mutu."

Magaji ya siffanta ta a matsayin mutum mai kokarin gaske. Ya yi addu'an Allah ya yafe mata kura-kuranta.

Marigayiyar ta kasance tsohuwar shugabar kungiyar mata yan jarida, shiyyar jihar Sokoto.

Tsohon shugaban kungiyar yan jarida NUJ na jihar Sokoto, Isa Abubakar Shuni, ya bayyana kaduwarsa game da mutwar yar jaridar.

Ta bar 'yaya uku.

Kara karanta wannan

Zamu Tabbatar Da Kun Samu Isasshen Mai Lokacin Zabe: NNPC Ya T

Yadda Kamfen PDP Ke Gudana Yau A Sakkwaton Shehu

Tawagar yakin neman zabe kujerar shugaban kasan Najeriya a zaben 2023 na jam'iyyar adawa ta PDP ta shiga cibiyar daular Islamiyya a yau Talata, 31 ga watan Junairu, 2023.

Alhaji Atiku Abubakar tare da tawagar kamfen jam'iyyar PDP sun kai ziyara kabarin mujaddadi Shehu Usmanu Danfodio.

Wannan na cikin ziyarar farko da suka kai gabanin zuwa filin taro.

Atiku ya yi addu'a wajen hubbaren.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Tags: