Zamu Tabbatar Da Kun Samu Isasshen Mai Lokacin Zabe: NNPC Ya Tabbatarwa INEC
- Shugaban hukumar INEC ya kai kuka wajen shugaban kamfanin NNPC kan matsalar tsadar mai
- Yan Najeriya sun shiga matsanancin tsadar man fetur tsawon watanni yanzu kuma har yanzu ana ciki
- INEC na hasashen cewa wannan rashin mai na iya zama babban matsala ga zaben shugaban kasan 2023
Abuja - Kamfanin man feturin Najeriya NNPCL ya bada tabbacin cewa na za'a fuskanci karancin man fetur lokacin zabe ba, saboda haka INEC ta kwantar da hankalinta.
Kimanin shekara guda kenan tun Febrairun 2022 yan Najeriya ke fuskantar tsadar man fetur da karancinsa.
A ranar Talata, 31 ga watan Junairu tawagar hukumar shirya zabe ta kasa INEC karkashin jagorancin shugabanta, Farfesa Mahmoud Yakubu, sun kai ziyara hedkwatar NNPC dake Abuja.
Wakilan na INEC sun tafi tattauna matsalar man da aka fama da shi ne a fadin kasar yanzu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
INEC ta bayyana cewa rashin mai na iya zama babban matsala ga zaben 2023 muddin ba'a magance matsalar ba, rahoton TheCable.
Martani kan hakan, Shugaban NNPC, Mele Idris Kyari, ya bayyana cewa ko kadan kada INEC ta damu za'a sama mata mai don amfani a lokacin zabe.
Yace:
"Zamu hada kai da direbobinku domin fahimtar wuraren da bamu da gidajen mai saboda mu bukaci wasu yan kasuwa su shigo lamarin don a samawa motocinku 100,000 da kuke fadi."
"Wannan ba abu mai wahala bane. Muna da gidajen mai; muna ko ina."
"Amma inda bamu da gidan mai, zamu tattauna da yan kasuwa saboda ku samu mai lokacin da kuke bukata."
Za mu bunkusa Arewa da kudin man da aka hako a Bauchi, Peter Obi
A wani labarin kuwa, Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar adawa ta Labour Party, Mr Peter Geregory Obi ya bayyanawa alummar Bauchin Yakubu abinda zai yi danyen man feturin da aka gani a jihar.
Obi ya laburta musu cewa zai ciyar da jihar da kuma yankin Arewacin Najeriya gaba da wannan arzikin mai.
Ya bayyana hakan ne yayin yakin neman zaben zaben jam'iyyar da ya gudana a filin wasa na Tafawa Balewa a Bauchi, babban birni Jihar Bauchi..
Peter Obi na cikin manyan yan takara 4 da ake ganin zasu taka rawar gani a zaben.
Asali: Legit.ng