Yanzu-Yanzu: Allah Ya Yi Wa Sarkin Dutse Muhammadu Sanusi Rasuwa

Yanzu-Yanzu: Allah Ya Yi Wa Sarkin Dutse Muhammadu Sanusi Rasuwa

  • Ranar bakin ciki ne a Najeriya a yayin da daya cikin manyan sarakunan arewacin kasar, Sarkin Dutse, Nuhu Muhammadu Sunusi II, ya rasu
  • Sanusi II wanda ya kwana biyu yana jinya, a cewar rahotanni, ya rasu ne a yammacin ranar Talata, 31 ga watan Janairu
  • An haifi sarkin mai daraja ta daya a shekarar 1945 a kauyen Yargaba da ke Dutse, babban birnin jihar Jigawa

Dutse, Jigawa - Mai martaba Sarkin Dutse, Alhaji Nuhu Muhammad Sunusi ya riga mu gidan gaskiya.

Auwal Danladi Sankara, kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Jigawa ya tabbatarwa BBC Hausa da rasuwar sarkin.

Sarkin Dutse
Allah Ya Yi Wa Sarkin Dutse Muhammadu Sanusi Rasuwa. Hoto: Photo credits: Comr Nura Nuhu Gwaramcy, Sa'adatu Baba Ahmad
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hakazalika, wakilin Legit.ng Hausa da ke birnin Dutse, babban birnin jihar Jigawa ya tabbatar da hakan bayan tuntubar wasu majiyoyi daga fadar sarki, amma sun nemi a sakaya sunansu.

Kara karanta wannan

Shawara ko Wasiyya: Abinda Marigayi Sarkin Dutse ya Fadawa Tinubu a Ziyarar da ya Kai Masa Satin da ya Gabata

Sarkin ya rasu ne a birnin tarayya Abuja bayan ya yi jinya.

Sarkin mai daraja ta daya a arewa maso yammacin kasar shine tsohon Chancellor na Jami'ar Jihar Sokoto.

Nuhu Muhammadu Sunusi II: Abin da muka sani game da marigayin sarkin Dutse?

An haifi Sarki Sunusi II ne a shekarar 1945 a kauyen Yargaba da ke Dutse, babban birnin jihar Jigawa. Ya halarci makarantar Dutse Elementary daga 1952 zuwa 1956.

Daga bisani ya samu satifiket din NCE daga jam'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, sannan digiri na farko da na biyu a bangaren kasuwancin kasa da kasa daga Jami'ar Ohio da ke Amurka.

Marigayin kuma ya yi difiloma a bangaren shirya aiki da fashin baki daga jami'ar Bradford da ke Birtaniya.

Jami'ar Fasaha ta Tarayya da ke Owerri, Jihar Imo ta bashi digirin digir-gir na karramawa.

Zaben 2023: Mene marigayi sarkin Dutse Muhammadu Sunusi II ya fada wa Tinubu?

Kara karanta wannan

Dalibar Jami'ar Abuja Ta Bankawa Dakin Kwanan Dalibai Wuta

A bangare guda, a baya Legit.ng ta rahoto cewa Sarkin na Dutse ya ce dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC ya cacanci ya jagoranci Najeriya duba da ayyukansa na baya a matsayin gwamnan jihar Legas da wasu abubuwa na siyasa.

Da ya ke magana a lokacin da Tinubu ya ziyarce shi a Dutse yayin da ya tafi yin kamfen a jihar, Sarki Sunusi ya ce dan takarar na APC ya taimaka wurin hada kan arewa da kudu don hada jam'iyyar siyasa mai karfi.

Wata sanarwa da Tunde Rahman, na ofishin watsa labarai na Tinubu ya aike wa Legit.ng ta ambato Tinubu na cewa:

"Na kasance mai bibiyan harkokin ka na siyasa. Lallai kai mutum ne wanda na yi imanin ka cancanci ka jagoranci kasar nan."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164