Bidiyon Kyakkyawar Budurwa Yar Arewa Da Dirarren Jiki Ya Dauka Hankali, Mijinta Ya Mata Liki a Taro
- Wata matashiya yar arewa mai ji da kyawun fuska da dirarren jiki ta yi fice a manhajar TikTok
- Wani bidiyo da ya yadu a dandalin ya nuno kyakkyawar matar tana jawabi a taron jama’a masu yawan gaske
- Yayin da take magana da dirarren jikinta a bayyane, mijinta ya fito cike da Alfa bari sannan ya fara lika mata bandir-bandir din kudi
Wani hadadden bidiyo da aka yada a soshiyal midiya ya nuno wani magidanci mai tsananin alfahari yana nuna kaunarsa ga kyakkyawar matarsa.
A wani bidiyo mai kayatar da zuciyar mai kallo, an gano dirarriyar matar tsaye a gaban jama’a tana koro jawabi kuma nan take mijin nata ya ji ta burge shi.

Asali: UGC
Bidiyon ya hasko mijin yana tunkaro kan mumbarin taron sannan ya yi wa matar tasa yayyafin kudi bandir-bandir inda ita kuma ta dunga murmusawa.
Jama’a sun gaggauta gano kyawun matar mai tsuma rai da kuma dirarriyar surar da take dauke da shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jama’a sun yi martani
@damien65 ya ce:
“Idan Ina da irin wannan a gida. Ba zan taba cin amanar matata ba.”
@khadee100 ta ce:
“Ta zo ta baje masa kayansa a bainar jama’a. Wasu mazabar basu da kishi gsky.”
@199abu ya ce:
“A ina suke samun irin wannan matan Ina bukatar daya cikin gaggawa.”
@laughinpio ta ce:
“Ba na jin turanci kuma ban san yadda ake turanci ba amma menene amfanin wannan kudaden dukka.”
@huawabello ta ce:
“Wannan yar arewar ta cika tsaf faaaaa.”
@beffjezos25 ya ce:
“A matsayina na inyamuri, zan iya auren Bahaushiya? Kawai Ina son yanayin yan arewa ne kuma wadannan mata sun hadu.”
Kalli bidiyon a kasa
Bidiyon yadda wasu matasa suka yi ruwan bandir-bandir din sabbin kudi a wajen biki ya ta da kura

Kara karanta wannan
Bidiyo:Matar aure ta Kama Mijinta Dumu-dumu da Budurwarsa a Wurin Cin Abinci, An Tafka Dirama
A wani labarin, mun ji cewa jama'a sun tofa albarkacin bakunansu bayan bayyanar bidiyon wasu matasa suna lika sabbin kudaden da CBN ya sauya a wajen wani biki.
Babban abun da ya tunzura yan Najeriya da dama shine ganin mutane na wahala don ganin sun samu kudin koda kadan ne amma babu su a gari sai ga shi wasu sun samu fiye da kima.
Asali: Legit.ng