Dalibar Jami'ar Abuja Ta Bankawa Dakin Kwanan Dalibai Wuta

Dalibar Jami'ar Abuja Ta Bankawa Dakin Kwanan Dalibai Wuta

  • Wata yarinya mai karatu a jami'ar Abuja wacce akafi sani da UniAbuja ta tayar da hankalin jama'a
  • Ana zaune kalau dalibar ta cinna wuta cikin dakin da take kwana tare da abokan karatunta
  • Daga bisani kuma tayi kokarin hallaka kanta inda dalibai suka kwace makami daga hannunta

Wata daliba mace a jami'ar birnin tarayya Abuja, a ranar Litnin, ta banka wuta dakin kwanan dalibai mata ana zaune kalau.

Punch ta ruwaito cewa bidiyon da ya bayyana ya nuna lokacin da dalibar ta cinnawa katifar kwanciyarta wuta kuma har ya kona dakinsu gaba daya kurmus.

Bidiyon ya nuna yadda yarinyar ta rike wuka tana barazana ga dukkan wadanda ke kokarin kashe wutar.

Abuja
Dalibar Jami'ar Abuja Ta Bankawa Dakin Kwanan Dalibai Wuta
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Yar Haya Ta Kashe Mai Gida Ta Hanyar Matse 'Ya'yan Marainansa A Ogun

Dalibai yan uwanta na zagaye da ita suna tsoron tana iya hallaka kanta.

Daga baya dai daliban suka samu nasarar kwace wukar daga hannunta kuma suka kashe wutar gudun kada ta haddasa gobara a makarantar.

Wata daliba ta mutu a tana mai shekaru 99

A wani labarin daban, Priscilla Sitieni wanda ita ce ake tunanin daliba mafi tsufa a makarantar firamare a Duniya, ta mutu tana ‘yar shekara 99 da haihuwa.

Wata jaridar kasar Kenya, The Standard newspaper ta fitar da rahoto cewa Gogo Priscilla kamar yadda jama'a suka fi saninta, ta bar Duniya.

Priscilla Sitieni ta mutu ne a ranar Larabar da ta gabata biyo bayan fama da ta yi da ciwon kirji, ta mutu ne a gidanta a kasar gabashin Afrikan.

Wata majiya daga dangin wannan tsohuwa sun bayyanawa manema labarai cewa har kwanaki ukun kafin ranar da za ta rasu, tana shiga aji.

Kara karanta wannan

Gaskiya daya ce: Fitaccen Sarki a Arewa ya ba 'yan siyasa shawari game da zaben gwamnoni

A dalilin wannan, hukumar nan ta UNESCO ta yaba mata, tace dattijuwar ta zama abin yin koyi.

Da majalisar dinkin Duniya tayi hira da ita, dattijuwar tace ta koma aji ne domin ta karfafawa matan Kenya su koma makaranta bayan tara yara.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida