Sai Yanzu Ka San Za Ka Zagi Buhari, Atiku Ya Caccaki Tinubu

Sai Yanzu Ka San Za Ka Zagi Buhari, Atiku Ya Caccaki Tinubu

  • Atiku Abubakar na tuhumar Tinubu da munafurci kan abubuwan da shugaba Muhammadu Buhari ke yi
  • Tinubu dai na zargin shugaba Buhari da mukarabansa wajen yi masa zagon kasa ana fuskantar zabe
  • Za a gudanar da zaben shugaban kasa ranar 25 ga watan Febrairu 2023 tare da na yan majalisa

Alhaji Atiku Abubakar, ya tuhumci Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasan All Progressives Congress (APC) da munafurci, sai yanzu yake zagin shugaba Muhammadu Buhari.

Atiku ya bayyana hakan ne a tsokacinsa game da jawabin da Tinubu yayi a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun ranar Laraba.

Tinubu, a jawabinsa ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Buhari ta taso da lamarin sauya fasalin Naira da tsadar mai saboda mutane su wahala kuma su ki zabensa a zaben 2023.

Tinubu ya shaidawa taron jama’a cewa:

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Yi Zama da Zababbun Sanatoci da ‘Yan Majalisa, Ya Yi Maganar ‘Dan Takaransa

“Ba sa son wannan zaben ya faru. Suna son su durkusar da shi. Za ku bar su?
"Sun fara zuwa da wani uzurin babu man fetur. Kada ku damu, idan ma babu mai, za mu taka don kada kuri'unmu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Idan kun ga dama, ku kara kudin farashin man, ku boye man ko kuma ku sauya launin Naira, za mu ci zaben nan."

Tinubu
Sai Yanzu Ka San Za Ka Zagi Buhari, Atiku Ya Caccaki Tinubu
Asali: Facebook

Jawabin Atiku

Martani kan hakan, Atiku ya fitar da jawabi ta hannun hadiminsa, Phrank Shaibu, rahoton DailyTrust.

Atiku yace:

"Saboda fusata ya kasa hana sabon tsarin daina yawon Naira da kuma sauya fasalin Naira da bankin CBN da akayi don dakile sayen kuri'u da inganta zaben wata mai zuwa, dan takaran shugaban kasa jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, ya fara kuka."

Kara karanta wannan

Na boye ya ya bayyana: Jigon APC ya yi sakin baki, ya fadi dalilin nasarar Bola Tinubu

"Duk da cewa dukkan jam'iyyun siyasa 18 wannan doka ta CBN ya shafa, Tinubu ne kadai ya gigice. Hakazalika ya fusata shugaba Muhammadu Buhari bai son zuwa kamfensa."

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida