Kudin Da Aka Karba Na Haraji A Shekara Shida Biliyan 378.7 Ba Ma Kai Tiriliyan Guda Ba
- Gwamnann babban bankin kasa ya mayar da martani kan zargin da gudaji kazaure yayi na batan wasu kudade
- A waccar shekarar data gabata ne dai gudajin yayi wannan zargin, inda yace akwai sama da tiriliyan N80 da doriya da suka bata
- Fadar shugaban kasa dai ta musanta zargin in da tace zargin gudajin bashi da tushe balle makama
Abuja - Babban bankin kasa CBN, ya ce kudin da aka karba na harajin fito a shekara shida da suka shude biliyan 378.7 ne.
Gwamnan da babban bankin kasa Godwin Emefiele ne ya bayyana haka gabanin kammala taron kwamitin da kula da tsare-tsaren kudi
A watan disambar shekarar da ta gabata, jaridar Premium Times ta rawaito, cewa dan majalisa Gudaji Kazaure, ya zargi wasu hukumomin gwamnatin tarayya da wofantar da kudi kusan triliyan N89.09 a matsayin kudin fito.
Dan majalissar wanda ya ke wakiltar kananan hukumomin Roni, Gwwiwa da Yankwashi a jihar jigawa ya zargi hukumomin da yiwa gwamnatin kasa zagon kasa, bayan da kwamitin sa wanda Buhari ya nada kan bincike kan kudin fito.
A wani martani da fadar shugaban kasa ta mayar, wanda babban mai Magana da yawun shugaba Buhari, Garba Shehu, ta bayyana zargin a matsayin marar tushe balle makama.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Martanin Gwamnan Babban Bankin Kasa
A ranar talatar nan ne dai gwamnann babban bankin kasa Godwin Emefiele ya maida martani kan abunda Gudajin ya zarga.
"Babban bankin kasa bazai yi magana kan cece kuce ba, mun rubutawa bankuna su fada mana nawa suka karba kan kudin fito daga 2016 zuwa yanzu" in ji gwanan bankin"
2023: Tinubu Ya Gana Da Malaman Addini Na Arewa Maso Gabas, Ya Sha Alwashin Kamanta Adalci Da Gaskiya
"Gaba daya jarin bankunan kasuwancin kasar nan tiriliyan N71 ne, yayin da kuma kudin da suke a cikin bankunan triliyan N44.49 daga 2016 zuwa yanzu, abinda suka karba kuma na kudin fito, biliyan N378,686
Kuma gaba daya a cikin wannan kudin, hukumar kula da haraji ta kasa FIRS, ce ta kawo kaso mafi tsoko wanda adadinsa yakai biliyan N226.451 kaga kenan saura biliyan N144 din sauran bankuna ne suka kawo ta, a martanin gwamnan babban bankin. Inji jaridar The Cable.
To wanne bankin ne yafi kawo kudin?
Ya ce bankin da ya fi kowanne a cikin wadannan bankunan kawo kudin fito shine bankin First Bank, wanda ya kawo kusan biliyan N71
Gwamnann babban bankin kasa CBN, yace sun sanya kwararrun masu bincike, kan su bincika abun da bankin ya kawo musu.
"Idan akwai abubuwan da basu kawo mana ba, to su zasu tabbatar mana"
Asali: Legit.ng