Kano: Matasa Biyu Sun Rasa Rayukansu Bayan Fadawa Sokaway a Kasuwa
- Matasa biyu masu shekaru 17 da 27 sun rasa rayukansu a sakamakon shiga masan bandaki da suka yi a kasuwar Sabon Gari da ke Fagge a Kano
- An gano cewa, mai shekaru 27 din ne ya fara shiga don yin wani gyara amma ya kasa fitowa, abokin aikinsa mai shekaru 17 ya kai masa dauki amma suka rufta ciki
- Hukumar kashe gobara ta jihar ta sanar da cewa, zafin wurin tare da rashin iska ne yayi ajalinsu tunda an tsamo su tare da kai su asibiti amma aka tabbatar da mutuwarsu
Kano - Maza biyu, mai shekaru 17 da mai shekaru 27 sun rasa rayukansu a cikin masan bandaki da ke kasuwar Sabon Gari a karamar hukumar Fagge ta jihar Kano a ranar Asabar yayin da suka je bude wurin don saukaka amfani da shi.
Kakakin hukumar kwana-kwana na jihar, Alhaji Saminu Abdullahi, ya bayyana cewa lamarin ya faru a Kano ranar Lahadi da dare, jaridar Vanguard ta rahoto.
Ya sanar da cewa, mai shekaru 27 din yana aiki cikin masan yayin da ya kasa fita kuma abokin aikinsa mai shekaru 17 ya shiga cikin katon ramin don ceto shi amma duk suka makale.
“Mun samun kiran gaggawa kan faruwar lamarin kuma mun gaggauta aika tawagar cetonmu zuwa wurin.”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
- Yace.
Ya kara da cewa, hukumar kashe gobarar ta fito da dukkansu basu san inda kansu yake ba kuma an kai su asibitin Murtala Muhammad inda likita ya tabbatar da mutuwarsu.
Abdullahi ya bayyana cewa an mika gawawwakinsu hannun ‘yan sandan da ke yankin Sabon Gari.
Ya alakanta mutuwarsu da tsananin zafi da kuma rashin iska a cikin masan.
Kamar yadda wani 'dan kasuwa mai siyar da takalma da jakla a kasuwar mai suna Malam Labibu ya bayyanawa wakiliyar Legit.ng Hausa, yace ya ji labarin amma lamarin ba ta bangarensu ya faru ba.
"Ta can wurin shagonsu Alhaji Manniru ne, ba ta nan bane. Sun je gyara amma ashe ajali ne ya kai su wurin. Su biyu ne kuma duka babu wanda ya kai shekaru 30 a cikinsu.
"Tabbas na samu labarin cewa mutane biyu sun je gyara sokaway din gidan wanka suka rassa rayukansu.
"Da yawa wuraren su kan yi taushi ne ta yadda kasar wurin ba ta iya rike su idan sun zo fita, ina ga hakan ne yayi dalilin kasa fitowarsu.
"Sannan kuma babu iska ga tsananin zafi, dole kuwa a rasa rai a irin wannan manyan ramukan."
- Ya tabbatarwa da Legit.ng Hausa.
Iyayen budurwa sun ki karban kayan aure saboda doya daya ta karye
A wani labari na daban, matashi daga jihar Imo ya bayyana yadda iyayen budurwar yayansa suka ki karbar kayan aure saboda doya daya cikin 400 da suka kai ta karye.
Sun ce dole ne ya je ya siyo wata ko kuma ba zasu bashi aure da karyayyar doya cikin dukiyar aure ba.
Asali: Legit.ng