Kotu Ta Yankewa Matashi Hukuncin Kisa Kan Satar N57,000

Kotu Ta Yankewa Matashi Hukuncin Kisa Kan Satar N57,000

  • Bayan shekara da shekaru ana shari'a, kotu ta yanke hukunci kan dan fashi da makami a Legas
  • Mutumin da aka kama da laifi ya yi amfani da almakashi wajen kwace kudin wata mata N57,000
  • Kotu ta yanke masa hukuncin kisa kuma ta yi addu'an Allah yayi masa rahama

Legas - Wata kotun laifuka na musamman dake karkashin jagoranin Alkali Mojisola Dada ta yankewa wani mutumi, Chidozie Onyinchiz, hukuncin kisa ranar Talata bisa laifin yiwa wata mata fashin N57,000.

Matar da ya yiwa fashin mai suna Mrs Veronica Uwayzor malamar jinya ce a jihar Legas.

Alkali Dada ta bayyana cewa lauyoyin gwamnati sun tabbatar da laifin fashi da makami, yaudara da kuma kasancewa mamban haramtacciyar kungiya, kan mutumin.

Jami'an hukumar yan sandan Igando jihar Legas suka damke Chidozie, rahoton TheNation.

Kara karanta wannan

Haren-haren da ake kaiwa cikin daji mata da yaran Fulani kawai ake kashewa, Gumi

Court
Kotu Ta Yankewa Matashi Hukuncin Kisa Kan Satar N57,000
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Alkalin tace:

"Wanda ake zargin ya bayyana cewa matar ta nuna shi a matsayin daya daga cikin mazaje biyu rike da almakashin da suka kwace jakarta da kudi N57,000 a Akesan Bus Stop."
"Chidozie Onyinchiz ya amince inda yace: 'wannan shine karon farko da zan so sata a Akesan. Na shiga kungiyar asirin Eiye a 2009 amma ban taba kashe kowa ba."
"Hujjan da aka gabatar gaban kotun nan na da yawa kuma na kama shi da laifin da ake tuhumarsa da su," Alkalin ta kara.
"Saboda haka an yanke masa hukuncin kisa. Allah yayi masa rahama."

Yadda aka kamasu

Lauyan gwamnatin jihar, Mrs Afolake Onayinka ya bayyana cewa mutumin da suka aikata wannan laifi tare da shi, Endurance Ediri, ya gudu tun ranar 12 ga Agusta, 2018.

Onayinka ya kara da cewa bayan kwacewa matar jaka, Chidozie da abokinsa Endurance sun gudu cikin wani coci.

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Kama Mutum 33 Kan Kisan Basarake a Jihar Arewa

Sai al'ummar cocin suka tona musu asiri har aka samu nasarar kama Chidozie, amma Endurance ya gudu.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida