Babu Shugaban Kasan Da Ya Kashe Fulani A Najeriya Irin Buhari, Sheikh Gumi

Babu Shugaban Kasan Da Ya Kashe Fulani A Najeriya Irin Buhari, Sheikh Gumi

  • Sheikh Ahmad Mahmoud Gummi ya magantu kan lamarin tsaron Najeriya a hirarsa da wata jarida
  • Gumi dai tuni ya dakatad da shirin kokarin sulhu tsakanin yan bindiga da gwamnatin Najeriya
  • Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya ce babu wata maganar sulhu da yan bindiga, kawai a kashesu

Shahrarren Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana cewa babu shugaban kasan da ya kashe Fulani ba gaira, ba dalili irin Shugaba Muhammadu Buhari.

Malamin ya shahara wajen ganin an yi sulhu tsakanin gwamnati da tsagerun yan bindigan daji masu garkuwa da mutane.

Ya yi wannan jawabi ne yayin wata da yayi da jaridar Vanguard.

Gummi
Babu Shugaban Kasan Da Ya Kashe Fulani A Najeriya Irin Buhari, Sheikh Gumi Hoto: Sheikh Ahmad Gumi
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sheikh Gumi ya yi bayanin yadda aka kafa kungiyar Ansaru wacce mambobinta suka kai mumunan hari kan jirgin kasan Abuja/Kaduna inda suka hallaka mutum 8 kuma suka debe gommai.

Kara karanta wannan

Ban Ba Yan Najeriya Kunya Ba, Inji Buhari Yayin da Yake Yi Wa Tinubu Kamfen

Hakazalika ya yi watsi da maganar da ke yaduwa cewa Shugaba Buhari na nuna bangaranci kuma bai son hukunta kabilarsa, Fulani, da Musulmai.

Gumi yace ai sai dai akasin haka, babu abinda Buhari ya yiwa kabilarsa.

A cewarsa:

"Mutane na gurgun fahimta. Idan akwai shugaban kasan da ya kashe makiyaya wadanda basu ji, basu gani ba, Buhari ne. Duk hare-haren nan da ake kaiwa, mutane, mata da yara ake kashewa."
"Amma lokacin da muka fito, bamu da komai - kuma babu wanda ya shirya sauraron mu. Har da yan jarida."

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida