Matashi Ya Sauya Gidan Iyayensa a Kauye, Ya Gina Masu Katafaren Gida Na Zamani
- Wani matashi dan Najeriya ya sha ruwan yabo a soshiyal midiya bayan ya nuna sabon gidan da ya kerwa iyayensa
- Bayan ya nunawa masu amfani da soshiyal midiya tsohon gidan da ya taso a ciki, matashin ya ce ya mallakawa ahlinsa wannan katafaren ginin
- Mutane sun bayyana cewa yana da yancin yin tinkaho da wannan nasarar da ya samu saboda abun da ya aikata ba karami bane
Wani matashi dan Najeriya, @teekay_love, ya wallafa wani bidiyo da ya burge mutane da dama a soshiyal midiya yayin da ya bayyanawa duniya katafaren gidan da ya kerawa iyayensa.
A cikin bidiyon da ya yadu, dan albarkan ya nuna tsohon gidan iyayensa a kauyen, yana mai sanar da mutane cewa a wannan gidan ne suka raine shi har ya girma.
Da ya gwangwaje iyayensa da hadadden gida
Yan sakanni da fara bidiyon, an Haskins sabon gidan da ya gina masu dauke da katan ‘gate’. Abun ya burge mutane da dama.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Matashin ya fada ma mutane cewa kada su taba mantawa da masoyansu da wadanda suka raine su. Da dama sun yi fatan zama irin shi wata rana.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama’a sun yi martani
king_samn38 ya ce:
“Ka yi tinkaho fa ba abu mai sauki bane...na taya ka murna.
Ya yi martani:
“Nagode dan uwa, Nagode dan uwa.”
Gifty ta ce:
“Hatta mahaifin ka ya yi kokari a nashi lokacin.”
ziwoya ya ce:
“Allah zai ci gaba da yi maka albarka.”
Sassy ta ce:
“Allah ya yi maka albarka, yaranka za su yi maka abubuwan alkhairi a rayuwa da izinin ubangiji.
__PoshneksNnekky11 ya ce:
Dan Najeriya Ya Kama Kifi Mai Launin Ruwan Gwal, Ya Nemi Sanin Darajarsa Kafin Ya Cinye, Bidiyon Yadu
“Ka daga kafadunka dan Allah ka tabbata dukka biyun ka daga dan Allah ina taya ka murna.”
Dankareren gidan Dino mai kama da aljannar duniya ya haddasa cece-kuce
A wani labarin kuma, mun ji cewa sanata Dino Melaye ya saki bidiyon katafaren gidansa da ke mahaifarsa ta jihar Kogi.
Katafaren gidan na dauke da filin wasa inda ake buga kwallo, kwallon tebur da kuma wasan raga, akwai kuma mujami'a a ciko.
Sai dai mutane da dama na ganij an yi almubazaranci wajen gina gidan.
Asali: Legit.ng