Yadda Wasu Suka Hadu Twitter Yanzu Maganar Da Ake An Sa Ranar Daurin Aure

Yadda Wasu Suka Hadu Twitter Yanzu Maganar Da Ake An Sa Ranar Daurin Aure

  • Kaji wani rabo fa, yadda wasu ma'aurata suka ghadu a Twitter sukai aure, a kasa da sati biyu da suka gabata
  • Sanadin zobo da kunun ne suka hada wannan zumuncin da ba wanda zai iya raba shi sai Allah
  • Masu korafi dai an damesu ta asusun tura sakonsu wannan sai ya zame musu izina wata suma suna da rabo

Katsina - Wani abin ta'ajibine mai cike da sarkakiya ya faru a kafar Twitter, in da wasu suka dace da juna sukai aure.

Sabida ci gaban zamani da yadda fasahar sadarwa ta saukakawa mutane abubuwa da yawa, yasa yanzu jama'a suka rungumi siyayya wato siye da siyarwa a kafar.

Sutura, tufafe, ababen yau da kulum da duk wani abu da zaka iya alkantawa ana siyansa ko siyarwa yanzu ana yinsa ta kafar sadarwar zamani.

Kara karanta wannan

Riba biyu: Daga siyan Zobo mai sanyi, matashi ya yi wuf da mai talla a Twitter, jama'a sun yi mamaki

Twitter
Yadda Wasu Suka Hadu Twitter Yanzu Maganar Da Ake An Sa Ranar Daurin Aure Hoto: Twiiter
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda abun ya faru

Wata ce mai suna @ammabature wanda asalin sunanta shine Aisha Sunusi Bature ce ta wallafa a shafinta na Twitter, cewa:

"ikon Allah kwastomana zai zama mijina"
"Daga siyan su zobo, da kunu aya da sauransu, yanzu zance sa mana rana ake"

Wanda ta auran mai suna Muhammad Sani Yawale, ya tura mata sako ne kai tsaye yace:

"Zan iya samun zobo da kunun aya mai sanyi, kafin na rufe wannan sakon ki najye min lamabar wayarki"

yau kimanin sati biyu kenan da daura auren a cikin garin Katsina a ranar 7 ga watan Janairun shekarar nan da muke ciki.

Ba wai ga iya Twitter ba, hatta sauran kafafen sadarwar na zamani, an samu auratayya da kuma sannayar juna a tsakani, musamman ma kafar Facebook, Instagram da sauransu.

Kara karanta wannan

Gobarar Titi: Yadda Wani Saurayi Ya Samu Dubu N150 Kan Budurwarsa Da Ta CInye Masa Kudi

Akwai wani tsari da kwanan ma ya shigo wanda masu amfani da wadannan kafafen suke fada da sunan "Hide my ID" wato kar a bayyana wanda ya turo, inda zaka ga mutum ya yi takaitaccen bayanin waye shi, sannan kuma ya nuna kalar mijin ko mata da ya bukata ya aura.

Masu Amfani da kafdafen sadarwa sun yi sharhi kan wannan abun da ya faru.

Masu amfani da shafin Twitter sunyi sam barka gami da addu'oin fatan zaman lafiya ga wadanan ma'auratan

@usman zanna yace

"na taya ku murna, Allah ya sanya alkhairi ya bada zaman lafiya"

@ummaali kuwa cewa tace:

"A matsayinmu na yan kungiyar masu saida zobo ta kasa muna taya ku murna

@Abumazida kuwa wata magana yayi yace:

"Lalle ke kam kinga albarka a zobo, inda addu'ar Allah ya baku zaman lafiya

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida