Fitaccen 'Dan Kasuwar Zaria, Alhaji Bako Zuntu, Ya Kwanta Dama

Fitaccen 'Dan Kasuwar Zaria, Alhaji Bako Zuntu, Ya Kwanta Dama

  • Fitaccen 'dan kasuwar garin Zaria, Alhaji Usman Bako Zuntu, ya kwanta dama yana da shekaru 84 a duniya
  • 'Dan kasuwan fitaccen 'dan kwangila ne kuma ya kasance shaharraren dillalin kayayyakin masarufi a Zaria
  • Ya rasu da asubahin ranar Juma'a bayan doguwar jinya da yayi fama da ita, ya bar matan aure biyu da 'yaya 26

Zaria, Kaduna - Allah ya yi wa Alhaji Usman Bako Zuntu, fitaccen 'dan kasuwar garin Zaria a jihar Kaduna, rasuwa.

Alhaji Bako Zuntu kamar yadda aka san shi, gogaggen 'dan kasuwa ne kuma 'dan kwangila mai shekaru 84 a duniya kafin rasuwarsa.

Alhaji Bako Zuntu
Fitaccen 'Dan Kasuwar Zaria, Alhaji Bako Zuntu, Ya Kwanta Dama. Hoto daga Malam Genty Zaria
Asali: UGC

Kamar yadda iyalan mamacin suka tabbatar, ya amsa kiran Ubangiji ne da asubar ranar Juma'a a fitaccen asibitin kudi na garin Zaria, Al-Madina da ke GRA bayan fama da yayi da doguwar jinya.

Kara karanta wannan

Kwamandoji Abu Ubaidah da Malam Yusuf Tare da Mayaka 40 na Boko Haram Sun Sheka Lahira Bayan Luguden NAF

Tsohon da yayi shekaru 84 a duniya yana daga cikin manyan 'yan kwangila kuma ya shahara a dillanci kayan masarufi a kamfanin PZ.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Haifaffen garin Zunti ne a karamar hukumar Kubau ta jihar Kaduna amma mazaunin Unguwar Magume a Tudun Jukun da ke Zaria duk tsawon rayuwarsa.

A tsawon rayuwarsa, Bako Zuntu ya kasance babban manomi kuma hamshakin mai arziki da ke tallafawa marasa karfi.

Ya rasu ya bar matan aure biyu da 'ya'ya 26 da ya haifa tare da jikoki masu tarin yawa.

An jana'izar marigayin a babban Masallacin Juma'a na Foliteknik ta Nuhu Bamalli mai kallon madaba'ar buga littatafai ta Gaskiya.

Legit.ng Hausa ta samu damar zantawa da wasu makwabtansa da wadanda suka san fitaccen 'dan kasuwar Zaria da ya kwanta dama.

Habibu Musa, makwabcin marigayin yace:

"Muna kuka tare da alhinin mutuwar dattijon kirki mai tausayin marasa karfi. Tabbas yayi rayuwa mai kyau don haka hatta tsufansa mai kyau yayi.

Kara karanta wannan

Jami'an NSCDC Sun Damke Mai POS da 'Yan Bindiga Suka Girke Yana Musu Hada-hadar Kudi

"Allah yayi masa albarkar 'ya'ya da jikoki kuma muna fatan su amfani al'umma kamar yadda mahaifinsu ya ke amfanar jama'ar Annabi."

Hajiya Mairo da ke gidan mahauta kusa da gadar Bako Zuntu tace:

"Ni dai tun da aka auro ni aka kawo ni layin nan na san gidan marigayin. Ban taba jin abokin fadansa ba. A kowanne lokaci alherinsa nake ji. Ina masa fatan Allah ya bashi damar amsa tambayar kabari. Allah ya amfana zuri'arsa."

Mata da miji da yaransu sun kone a gobara

A wani labari na daban, wata mata tare da mijinta da yaransu sun kurmushe a wata mummunar gobara a Zaria.

Lamarin ya ritsa da su cikin dare kuma ya faru a yankin Low Cost da ke Zaria.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng