Yan Najeriya Sun Yiwa Dan Shekara 16 Mai Tuka Adaidaita Sha Tara Ta Arziki, Sun Hada Masa N82,000

Yan Najeriya Sun Yiwa Dan Shekara 16 Mai Tuka Adaidaita Sha Tara Ta Arziki, Sun Hada Masa N82,000

  • Wasu yan Najeriya sun nuna karamci ga yaro dan shekaru 16 da ke tuka adaidaita sahu don neman na kai
  • Labarin shi ya dauki hankalin wani shahararre a soshiyal midiya @jojoflele ya wallafa shi a shafinsa na soshiyal midiya
  • Zuwa yanzu an tara masa N82,000 don ya koma makaranta ya ci gaba da karatunsa na sakandare

Yan Najeriya sun sake mika karamcinsu ga wani matashin yaro dan shekaru 16 wanda ke sana’ar tuka adaidaita sahu.

A wani bidiyo da shafin @jojooflele ya wallafa a Instagram a ranar 18 ga watan Janairu, an gano cewa yaron ya shiga sana’ar tuka adaidaita ne saboda talaucin gidansu.

Matashi ya samu tallafi
Yan Najeriya Sun Yiwa Dan Shekara 16 Mai Tuka Adaidaita Sha Tara Ta Arziki, Sun Hada Masa N82,000 Hoto: @jojoflele
Asali: Instagram

An tara masa kudi

Bayan labarin ya ja hankalin @jojoflele, shahararre a soshiyal midiya, sai ya nemi a hada masa kudi ta shafinsa don ya shiga makaranta.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Tono Asalin Matsala, Ya Fadi Abu Ɗaya Tak Da Ya Kawo Yan Bindiga Arewacin Najeirya

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bayan wannan bukata tasa, yan Najeriya sun nuna masa karamci kuma zuwa yanzu sun tara masa N82,000.

Kalli bidiyon a kasa :

Jama’a sun yi martani

@seyufunmi945 ta ce:

“Godiya gareka da wannan aminci naka, Allah ubangiji ya albarkace ka sosai da sosai.”

@cullinian_vintage ya ce:

“Ba zo taba talauci ba duba da yadda yake tasowa...godiya gareka jojo.”

@kingprincee4 ya ce:

“Godiya gareka jojo, dariyarka kadai dala biliyan 1 ne. Allah ya albarkace ka har abada.”

@mandaibga ya ce:

“Fuskar mahaifiyar yana sacewa mutum gwiwa kamar ba abu mai kyau ake yi ba, amma ta dara lokacin da ta ga kudi. Mutane kooo. Allah ya maki albarka yarinya.”

N56,163 nake samu kullun a matsayin albashi, Yar Najeriya da ke zama a UK

A wani labarin, wata matashiyar budurwa yar Najeriya da ke zaune a kasar Birtaniya ta bayyana yawan albashin da take karba a kullun kwanar duniya.

Kara karanta wannan

Ba Zan Yi Lefe Ba: Matashi Na Neman Karin Mata Ta Biyu, Ya Ce Zai Biya Sadakin Miliyan N1 da Wasu Sharudda

Budurwar mai suna Ihemeson Akunna wacce ke aikin kula da mutum ta ce a duk kwanan duniya, ana biyanta albashi fam 100 wanda ya yi daidai da N56,163 na kudin Najeriyan kuma ta ce tana matukar alfahari da aikin nata.

Ta bayyana hakan ne yayin da take martani ga masu mata ba a a kan irin sana'ar da take yi a can kasar Birtaniyan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng