Jerin Alkalan Kotun Shari'a Da Ma'aikata 19 Da Suka Sace N580m na Magada a Kano
Labari ya gabata kan yadda wasu Alkalan kotun shari'a biyu da tare kashiya mai ajiyan kudin kotu da wasu mutum 16 suka sace kudi Naira milyan dari biyar da tamanin da digo biyu.
An gurfanar da su gaban kotun majistare inda suka musanta zargin da ake musu.
Alkalin kotun ya hana belinsu kuma ya bada umurnin jefasu gidan gyara hali zuwa watan Febrairu da za'a koma zama.
Ga jerin sunayensu:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
- Bashir Kurawa
- Saadatu Umar
- Tijjani Abdullahi
- Maryam Jibrin-Garba
- Shamsu Sani
- Hussaina Imam
- Sani Ali Muhammad
- Sani Buba-Aliyu
- Bashir Baffa
- Garzali Wada
- Hadi Tijjani Mu’azu
- Alkasim Abdullahi
- Yusuf Abdullahi
- Mustapha Bala Ibrahim
- Jafar Ahmad
- Adamu Balarabe
- Aminu Abdulkadir
- Abdullahi Zango
- Garba Yusuf
Yadda akayi a kotu
A zaman kotun, lauyan gwamnati Mr Zahraddeen Kofar-Mata ya bayyana cewa hukumar yaki da rashawan jihar Kano ta samu rahoton badakalar daga wajen ma'aikatar shari'a ranar 20 ga Agusta, 2021.
Ya ce tsakanin 2020 da 2021, daya daga cikin wadanda ake zargi Hussaina Imam, wacce mai ajiyan kudi ce a kotun daukaka kara ta hada baki da wasu mutum hudu wajen buga jabun takardan kotun.
Yace:
"Sun buga jabun sa hannun mutum biyu a akawunt na bankin kotun dake Stanbic IBTC bank 0020667440 kuma suka sace N484 million."
Ya kara da cewa tsakanin 2018 da 2021, sun sace kudi N96.2 million ta hanyar buga jabun takardun mutuwar wasu ma'aikatan gwamnati 15 don kwashe kudin fansho.
Yace:
"Hukumar fanshon jihar Kano ta sanya kudi N96.2 million cikin asusun bankin kotun daukaka kara ta shari'a."
"Wadannan mutane suka sace kudin da sunan kotunan shari'a takwas dake karkashin kular kotun daukaka karar ba tare da izinin gwamnati ba."
Asali: Legit.ng