'Dan Najeriyan da ya Warware Matsalar Lissafi ta Shekara 30 a Japan Yanzu Yana Hada Motoci

'Dan Najeriyan da ya Warware Matsalar Lissafi ta Shekara 30 a Japan Yanzu Yana Hada Motoci

  • Wani 'dan Najeriya ya bayyana sunansa ga duniya yayin da ya karya kwarin shekaru 30 a tarihin lissafi a kasar Japan
  • A lokacin yana 'dalibi a jami'ar Tokai da ke Tokyo, ya magance matsalar lissafi da kwararru a fannin lissafi suka kasa a sama da shekaru 30
  • Nasarorin da ya samu sun janyo masa jinjina da dama a kasar Japan gami da zama dalibin da yafi kowa hazaka a tarihin jami'ar

'Yan Najeriya sun yi fice a hazaka da kwazo idan suka tafi kasashen ketare don yin karatu.

A karo daban-daban, mun ga 'yan Najeriya a matsayin daliban da suka fi kowa hazaka gami da fitowa da sakamakon da yafi na kowa kyau a wasu manyan jami'oin Turai, Arewacin Amurka da Asiya.

'Dan Najeriya
'Dan Najeriyan da ya Warware Matsalar Lissafi ta Shekara 30 a Japan Yanzu Yana Hada Motoci. Hoto daga @Africa_Archives
Asali: Twitter

Yanzu Ekòng yana kera motoci a kamfanin Nissan kuma da wasu kayyakin duk da mota mai amfani da wutar lantarki da ya kera da hannunsa.

Kara karanta wannan

Sabon salo: Daga ranar 25 ga wata na daina karbar tsoffin Naira, inji dan kasuwa a jihar Arewa

Irinsu Farfesa Wole Soyinka, Adebayo Ogunlesi, Bennet Omalu da sauransu su ne misalin 'yan Najeriyan da suka kafa tarihi a duniya saboda irin kwazo da baiwar da suke da shi a ilimi, baiwa, kimiyya da sauransu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ufo Ekong, wani matashi 'dan Najeriya ya shiga jerin sunayen tarin wadannan hazukan da suka wakilci Najeriya wanda ya kafa tarihin warware wata matsalar lissafi da kwararru a fannin suka gaza warwarewa sama da shekaru 30 a jami'ar Tokai, Tokyo da ke Japan.

Wannan abun burgewa ya jawowa Ekong jinjina daga shugaban kasar, inda ya kammala karatun jami'ar a matsayin dalibin da yafi kowa kwazo.

Kamar yadda African Archives ta bayyana, Ekong wani kawataccen injinyan lantarki ne, wanda yanzu yake aiki gami da kera motocin ga babban kamfanin kirar motoci na Nissan.

A halin yanzu, Ekong na kera motoci masu amfani da wutar lantarki a kamfanin Nissan cikin Japan.

Kara karanta wannan

Jerin Matsaloli Jingim da ke Jiran Duk Wanda Zai Gaji Shugaba Buhari a Aso Rock

A watan Janairu 2023, Ekong ya samar da wasu kwararan kayyaki biyu, duk da wata mota mai amfani da lantarki da ya kera da hannunsa.

Ekong ya kammala digirinsa na biyu a kirar lantarki da kayan wuta da kuma digirin digirgir a kan kayayyakin wuta da tukin mota daga jami'ar Tokai wanda yafi kowa maki a tsawon shekaru 81 da kafa jami'ar zuwa yanzu.

Haka zalika, ya iya yaren Turanci, Japananci, Furansanci, Yarbanci, yaren Ibiobio ba tare da gargada ba.

Matar da tafi kowanne Bil Adama tsufa ta mutu

A wani labari na daban, wata mata mai suna Lucile Randon wacce aka fi sani da Sister Andre, ita ce mutum da tafi kowa tsufa a duniya, ta rasu tana da shekaru 118 a duniya.

Ita ce mutum mafi tsufa da cutar korona ta kama kuma ta warware a tarihin duniya shekarar 2020.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng