Na Cika Alkawaran Da Na Daukarwa Yan Najeriya - Inji Shugaba Buhari
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya gamawa Najeriya komai a yayin da wa’adin mulkinsa ke gab da cika
- Buhari a wata sanarwa daga kakakinsa, Femi Adesina, ya bayyana cewa ya cika alkawaran da ya daukarwa yan Najeriya musamman na yakar Boko Haram
- Shugaban Najeriyan ya kuma bayyana cewa zai bautawa Allah da Najeriya har zuwa ranar da zai bar karagar mulki
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya cika dukka alkawaran da ya daukarwa yan Najeriya na magance ta’addancin Boko Haram, farfado da tattalin arziki da yaki da rashawa.
A cewar kakakinsa, Femi Adesina, shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin wani taro da aka shirya don karrama shi a Damaturu, babban birnin jihar Yobe.
Shugaban kasar ya kai ziyarar aiki jihar Yobe a ranar Litinin, 9 ga watan Janairu, Daily Trust ta rahoto.
A wata sanarwa da ya fitar, Adesina ya ce Buhari ya kuma bayyana cewa babu wanda zai iya bata masa suna cewa ya azurta kansa a lokacin da yake kan karagar mulki, rahoton Vanguard.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Buhari ya magantu kan shirye-shiryensa idan ya sauka daga mulki
Buhari ya kuma bayyana cewa bai da niyan barin Najeriya idan ya kammala wa'adinsa a matsayin shugaban kasa.
Jawabin na cewa:
“Da yake jawabi a wani taron a daren ranar Litinin wanda aka shirya don karrama shi a Damaturu, babban birnin jihar Yobe, shugaban kasar ya sake shan alwashin bayyana Allah da Najeriya har zuwa ranarsa ya karshe a mulki da bayan haka.
“Ya shawarci yan Najeriya da su ci gaba da zama masu kishin kasa kamar yadda na sha fadi fiye da shekaru 30 da suka shige cewa bamu da wata kasar bayan Najeriya, ya zama dole mu ci gaba da kasancewa a nan tare da cetota a tare.”
Shugaban kasar ya kuma tabbatar da cewar zaman lafiya ya dawo jihohin da matsalar ta’addanci ya shafa a arewa maso gabas.
Ya kuma ayyana cewa ya cika alkawaran da ya daukarwa yan Najeriya yayin rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayun 2015.
Ya ci gaba da cewa:
“A arewa maso gabas, Allah ya taimake mu wajen kakkabe Boko Haram, tattalin arziki ya daga kuma wasu na yi mun tambaya game da nasarorin alkawarin da na dauka na yakar rashawa.
“Toh dai, a karkashin wannan tsari na yakar cin hanci da rashawa ba abu ne mai sauki ba. A lokacin da nake aikin soja a matsayin shugaban kasa, na rufe wasu mutane saboda kundin tsarin mulki ya ce dole ka bayyana kadarorinka kuma mutane sun gaza bayanin banbanci a kadarorinsu, na rufe su.
“A karshe, an rufe ni. Saboda haka, idan kana son hidimtawa kasar nan dole ka shirya na munanan abubuwa. Amma abu daya da nake godiya ga Allah shine cewa babu wanda zai iya shafa mun bakin fenti. Ban mallaki fili a wajen Najeriya ba kuma ina niyan zama a Najeriya idan na bar mulki."
Farin jinin APC a arewa ya koma kan Kwankwaso
A wani labari na daban, Abdulmumin Jibrin, tsohon dan mjalisar wakilai kuma jigo a jam'iyyar NNPP ya ce APC bata da sauran farin jini a arewa.
Abdulmumin ya ce gaba daya son da ake yiwa APC a yankin arewacin kasar ya koma kan dan takarar shugaban kasa na NNPP, Sanata Rabiu kwankwaso
Asali: Legit.ng