Ma’auratan Da Suka Shafe Shekaru 10 da Aure Har da Yara 2 Sun Gano Cewa Su Yaya da Kanwa Ne, Bidiyon Ya Yadu

Ma’auratan Da Suka Shafe Shekaru 10 da Aure Har da Yara 2 Sun Gano Cewa Su Yaya da Kanwa Ne, Bidiyon Ya Yadu

  • Wasu ma’aurata sun haddasa cece-kuce a soshiyal midiya sakamakon gano wani al’amari da suka yi game da alakar da ke tsakaninsu
  • Bayan shafe tsawon shekaru 13 tare a matsayin mata da miji, sun gano cewa su din yaya da kanwa ne
  • Jama’a sun martani kan bidiyon ma’auratan yayin da mutane ke maimakij me ya hana su bin diddiginsu kafin su yi aure

Wasu ma’aurata da suka shafe tsawon shekaru 10 da aure sun bayyana cewa su din yaya da kanwa ne a zahiri.

Ma’auratan yan kasar Amurka sun bayyana abun ban mamakin a wani bidiyo da ya yadu a TikTok wanda @stzyathletemo ya wallafa.

Ma'aurata
Ma’auratan Da Suka Shafe Shekaru 10 da Aure Har da Yara 2 Sun Gano Cewa Su Yaya da Kanwa Ne, Bidiyon Ya Yadu Hoto: TikTok/@stzyathletemo
Asali: UGC

Mijin wanda ya yi magana a madadin iyalin ya bayyana cewa sun yi aure a 2008 kuma aun haifi dansu na fari a 2011.

Ya bayyana cewa sun haifi yarsu ta biyu a 2015 kuma sun shafe tsawon shekaru 23 tare. Sai dai kuma, sun gani cewa su din jini ne a kwanan nan.

Kara karanta wannan

Ya Yi Sa’a: Matashiyar Baturiya Ta Kai Saurayinta Dan Najeriya Gida Don Iyaye Su Gani, Ta Rangada Masa Girki

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

kevinellis211 ya ce:

“Wannan abu na faruwa fiye da tunaninku!! Ina da abokai masu aure da a kwanan nan ne suka gano cewa su din jini ne.”

Ashley Blanks ta ce:

“Uwar rikona ta fada mani cewa kada na yarda magana ta fatar baki ya hada ni da duk wanda ya fito daga Mobile, Al saboda mahaifina na da yara cike da wurin.

Kaleepha888 ya ce:

“Shiyasa a zamanin da lokacin iyaye da kakanni ake saka su yin gwajin jini kafin su yi aure. Wannan ne dalili.”

Nupe_5 ya ce:

“Ina nufin a wannan gabar me Za ka yi? Ka rigada ka fada tarkon soyayya."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng