Gwamnatin Birtaniya Ce Ta Gayyaci Atiku: Kwamitin Kamfe Ta Martani

Gwamnatin Birtaniya Ce Ta Gayyaci Atiku: Kwamitin Kamfe Ta Martani

  • Sanata Dino Melaye ya aike sakon kar-ta-kwana game da jita-jitan rashin lafiyan maigidansa Atiku
  • Wani jigon jam'iyyar APC ya ce an garzaya da Atiku Abubakar Dubai saboda yana fama da rashin lafiya
  • Melaye ya ce Atiku Abubakar na cikin lafiya da aminci kuma Birtaniya ce ta gayyacesa

Dan takaran kujerar shugaban kasan Najeriya a zaben 2023 karkashin inuwar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya tafi Landan ne bisa gayyatar gwamnatin Birtaniya.

Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben jam'iyyar, Dino Melaye, ya bayyana hakan a ranar Lahadi.

Ya yi tsokacin ne mayar da martani ga Femi Fani Kayode wanda ya ce an garzaya da Atiku birnin Dubai don jinya.

Jaridar Tribune ta ruwaito Dino Melaye da cewa Atiku yana cikin koshin lafiya.

Kara karanta wannan

Ina Atiku Yake? Ya Sake Zuwa Dubai Kanin Likita, Kafarsa Na Ciwo: Fani Kayode

Dino and Atiku
Gwamnatin Birtaniya Ce Ta Gayyaci Atiku: Gwamnatin Kamfe Ta Martani
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce gwamnatin Birtaniya ta gayyacesa ne kamar yadda ta gayyaci Bola Ahmed Tinubu da APC da kuma Peter Obi na PDP.

A sakon WhatsApp, Melaye yace:

"Ku yi watsi da karerayin makaryata. Atiku na cikin koshin lafiya dari bisa dari."
"Gwamnatin Birtaniya ce ta gayyaci dan takarar kamar yadda ta gayyaci Tinubu da Peter Obi."

Dino Melaye na cikin wadanda suka yiwa Alhaji Atiku Abubakar rakiya zuwa kasar Birtaniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida