Abun Bakin Ciki: Dan Sanda Ya Kashe Mutum 2, Ya Raunata Wasu 3 a Katsina
- Wani mummunan labari da muke samu shine na mutuwar wasu mutane biyu a jihar Katsina
- Rundunar yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da kisan mutum biyu tare da raunata wasu uku da ake zargin jami'inta da yi
- Mummunan al'amarin ya afku ne a yankin Filin Kanada da ke jihar, kuma an kaddamar da bincike
Katsina - Duk da kiraye-kirayen da ake yi na neman a gyara fasalin hukumar yan sandan Najeriya jami'an rundunar na ci gaba da cin zarafin al'umma.
A ranar Lahadi, 1 ga watan Janairun 2023, wani jami'in dan sanda a jihar Katsina ya bindige wasu mutane biyu.
Abun da ya faru
A cewar wani rahoto daga jaridar Sahara Reporters, lamarin ya afku ne a yankin Filin Kanada da ke jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu matasa uku sun kuma ji rauni sakamakon harbin.
"Wani jami'in dan sanda ya harba da kashe mutum biyu, yayin da dan sandan ya kuma raunana matasa uku," cewar majiya.
Rundunar yan sanda ta tabbatar da lamarin
Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar, Isah Gambo ya tabbatar da lamarin ga Sahara Reporters.
Sai dai kuma ya ce ana kan gudanar da bincike don gano makashin saboda akwai sauran jami'ai tare da yan sanda a shingen binciken.
"Ina sane da lamarin amma ba za ka iya cewa mutane na ba saboda ba yan sanda kawai bane a wajen. Akwai sauran hukumomin tsaro a wajen wanda bana son ambatan suna.
"Lamarin na karkashin bincike da nufin gano ainahin wanda ya aikata laifin."
Hakan na zuwa ne yan kwanaki bayan wani ASP ya kashe wata lauya mai ciki, Misis Omobolanle Raheem a yankin Ajah da ke jihar Lagas.
A gefe guda, mun ji cewa kungiyar lauyoyin Najeriya ta ce za ta nemi a biya akalla naira biliyan 5 a matsayin diyya ga iyalan lauyar Lagas, Omobolanle Raheem, wacce aka kashe.
NBA ta kuma ce za ta bi diddigi a shari'ar ASP Drambi Vandi, wanda ya yi ajalin Misis Raheem a jihar Lagas a ranar Kirsimeti.
Marigayiyar da mijinta na a hanyarsu ta dawowa daga coci lokacin da mummunan al'amarin ya afku.
Asali: Legit.ng