Duk da Raguwar Arzikinsa, Dangote Ya Kare 2022 da Wata Babbar Nasara, Ya Ci Ribar N27.7bn a Watan Disamba
- Aliko Dangote ya kare 2022 da babbar riba yayin da ya lashe N27bn a watan Disamban shekarar da ta gabata
- Ribar da ya samu ta samo asali ne daga abin da kamfaninsa na siminta ya kawo da dai sauran hannayen jari
- A yanzu haka shine attajiri na 80 a duniya bayan da ya sauka daga na 76 a jerin attajiran na duniya a bara
Aliko Dangote na ci gaba da girbar riba a matsayinsa na attajirin da ya fi kowa kudi a Afrika.
Hamshakin attajirin ya zama na 80 a jerin masu kudin duniya, inda ya samu ribar $28.6m, kusan N27.7bn a watan Disamban da ta gabata, inji Bloomberg.
An ce attajirin ya samu wadannan kudade ne mafi akasari daga ribar da kamfaninsa na siminti ya samar a shekarar.
A halin yanzu, kamfanin simitin Dangote na da darajar N261 kan kowane hannun jari, kuma ta nan attajirin ke samun kudade da yawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dangote, dan asalin jihar Kano shi ke rike da kaso mai tsoka a hannun jarin kamfanin simintin Dangote tare da hannaye 27,642,637 ya zuwa Janairun 2022, inji rahotanni.
Dangote ya zama na 80 daga na 76 a jerin attajiran duniya
Duk da faduwarsa daga matsayi na 76 zuwa na 80, dukiyar Dangote ta kai $18.7bn, kadan ya hana ya iso attajirin Rasha, Alexei Mordashove.
Dangote dai kwandila ne a nahiyar Afrika, kuma kamfaninsa na samar da kayayyakin rayuwa na yau da kullum da yawa a duniya.
Kamfaninsa ne mafi girma wajen samar da siminti a nahiyar Afrika, inda ya samar da N1.38trn na kudin shiga a shekarar 2021.
Hakazalika, yana samar da sukari, mai, taki, taliya da sauran kayan masarufi da ake amfani dasu a Afrika.
Matatar man Dangote za ta warkar da ciwon wahalar man fetur a Najeriya
Ana kyautata zaton cewa, matatar man Dangote za ta fara aiki a watan Yunin 2023, kuma za ta bunkasa matsayin Dangote babu shakka.
A cewar rahotanni, matatar man za ta samar da tan miliyan 10 na man fetur, ta hanyar samar da ganga 65,000 a kowacce rana.
Ana sa ran, wannan matata za ta kawo karshen wahala da karancin man fetur da ake fama dashi a Najeriya na tsawon lokaci.
A shekarar da ta gabata, Dangote da Adenuga sun yi asarar kudade, yayin da Abdulsamad Rabiu ya kwashi riba da karin arziki.
Asali: Legit.ng