Malamai Sun Zane Ni Sosai Saboda Ina Gudun Zuwa Gonar Makaranta, In ji Buhari
- Shugaba Muhammadu Buhari ya tuno da irin rayuwar da ya yi a makaranta a lokacin da yake matashin saurayi
- Shugaban kasar Najeriya ya ce ya sha bulala sosai a hannun malamansa saboda ya kasance mutum mai gudun zuwa gonar makaranta a lokacin damuna
- Buhari ya ce malaman lokacinsu sun kasance jajirtattu masu sadaukar da kai da daukar dalibai tamkar 'ya'yan cikinsu
Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce an sha zane shi da bulala kan gujema aiki da gangan a gonar makaranta a lokacin da suke sakandare.
Buhari ya fadi hakan ne a cikin wani shiri mai suna 'Abubuwa na musamman game da Muhammadu Buhari’ wanda aka watsa a ranar Lahadi.
Da yake tuna zamanin da yake karatu a sakandare, shugaban kasar ya ce malamai a lokacinsu suna sadaukar komai nasu a kan aiki yayin da suke daukar dalibai kamar yaran cikinsu.
Ya kara da cewar malamai na yabama dalibai wadanda suka nuna kwazo yayin da suke ladabtar da wadanda suka yi akasin haka.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Jaridar The Cable ta nakalto Buhari na cewa:
"Malamai a lokacinmu jajitatu ne da sadaukarwa. Suna daukarmu tamkar yaransu. Idan ka yi kokari, za a yaba maka a aji, kuma idan ka yi rashin kokari, za a zane ka a mazaunanka yayin da fuskarka ke fuskantar bango.
"Babu yadda za a yi na manta da Mallam Abdul. Ya kasance mutum mai tsauro kuma baya wasa da bulala.
"A lokacin, bama son lokaci na damuna saboda dole mu je gonar makaranta. Kuma idan ka yi lattin zuwa makaranta, daga 6:00am zuwa 2:00pm za a zane ka a mazauninka; muna cire wandunanmu don sakon ya isa da yau. Daga cikin malaman da ba zan taba mantawa da su ba shine malamin mu na harshen larabci. Komai zafi baya taba zuwa aji ba tare da rawani ba. Duk mako, ana bamu ayoyi daga Al-Qur'ani da za mu karanto.
"Na sha zana sosai saboda a kulla-yaumin ina gudun zuwa gonar makaranta. Kuma idan ka yi fashin zuwa gonar makaranta, ba za bari ka fita lokacin wasa ba. Amma abun da na kan yi shine zuwa bandakin makaranta a wasu lokutan, zan ci tufa na lokacin da sauran mutane ke aji. Kuma babu mai mantawa da dukka wadannan."
Kwankwaso ya taimaka mani a lokacin tashin bam a Kaduna
A gefe guda, Buhari ya tuno da lamarin farmakin da aka kai masa a jihar Kaduna, shekara daya kafin ya zama shugaban kasar Najeriya.
Buhari ya kubuta ba tare da samun rauni ba a tashin bam wanda ya afku a kasuwar Kawo dake birnin Kaduna, hadimansa uku suka jikkata aka hanzarta kai su Asibiti.
Asali: Legit.ng