Mashahuran Mutane Da Sannannu Da Suka Kwanta Dama A Shekarar 2022
- Wannan shekarar an rasa mutane da dama wanda suka hada da masu fada aji da kuma sannannu
- An rasa wanda ya rike Nigeria a tsakanin shekara 1993 bayan da aka bashi rikon kwaryar kasar na wasu lokuta
- Baya ga cutar annobar korona da ta tafi da rayukan al'umma da dam wannan shekarar ma anga yadda shekarar tazo da rasa manyan-manyan mutane ba ma iya Nigeria ba harda Duniya gaba daya
Nigeria - Nigeria taga rashe-rashe da suka hada manyan mutane wanda suka bada gudunmawa mai tsoka wajen ci gaban Nigeria, da kuma wasu sannanu da sukai suna wajen harkokinsu na wasan kwakwayo ko kuma wani abu mai kama da haka.
An waiwaye tare da tariyar baya da zakulo sannannun mutane da suka rasu a shekarar nan da muke bankwana da ita a ciki da wajen Nigeria.
Olubadan of Ibadan, Oba Saliu Adetunji
Shugaban yankin yarabawa mai cikakken iko na daya Oba Saliu ya rasu ne a farkon wannan shekarar yana da shekara 93 a duniya, kuma shine sarkin Badun na 41.
Sidney Poitier
Shararren dan wasan diramar din nan na Amurka kuma mai bada umarni Sidney Oitier ya rasu yana da shekaru 93 a duniya
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ernest Shonekan
Ya rike Nigeria bayan da akai zaben shekarar Yuni na 1993 aka samu sabani, sai gwamnatin Babbangida ta bashi rikon kwarya kasar. Ernest Shonekan ya rasu yana da shekaru 85 a duniya
Ibrahim Boubacar Keita
Keita shine tsohon shugaban kasar Mali da ya shafe shekaru masu yawa akan karagar mulkin kasar, juyin mulkin shekarar 2020 ne ya hambarar da gwamnatinsa. Keita ya rasu yana da shekara 76 a duniya.
Festus Okubule
Na cikin tsoffi kuma mashahuran masu alkalancin wasan gasar kwallon kwafa a ciki da wajen Nigeria, ya rasu a ranar 5 ga watan Afirilu na wannan shekarar yana da shekaru 80 a duniya.
Alaafin of Oyo, Oba Lamidi Adeyemi
Na daya daga cikin masu fada aji a yankin yarabawa kuma dan sarautar yanki, ya rasu yana da shekara 83 a duniya a ranar 23 ga watan Afirilun shekarar nan
Gbenga Richards
Sannanne kuma kwarraren mai shirya wasannin diramar kudancin kasar nan musamman a karshe shekarun 1999 zuwa farkon 2000. ya rasu a watan Mayun wannan shekarar.
Shinzo Abe
Tsohon shugaban gwamnatin kasar japan, wanda yayi mulki tsakanin shekarar 2006 zuwa 2007 ya rasu yana da shekara 67 a duniya.
Ivana Trump
Ivana Trump matar tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ta rasu ranar 14 ga watan Yuni na Shekarar nan, kuma ta rasu tana da shekara 73 a duniya. Itace mahaifiyar manyan 'ya 'yan Donald Trump guda uku.
Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye
Queen Elizabeth
Shekarar 2022 zata zama a zukatan mutane sabida rasuwar Giwar ingila wacce ta kasance mafi dadewa a karagar mulkin masarautar. An sha dai yada jita-jita kan lafiyar sarauniya da abubuwan da suke damunta gabanin rasuwarta
Ta rasu tana da shekara 96 a duniya, kuma ta rasu da misalin karfe 3:10 na yamma a agogan kasar ingila a ranar 8 Ga watan Satumbar wannan shekarar a fadarta ta Balmoral
Bashir Mangal
Mataimakin kamfanin zirga-zirgan jiragen sama na Max Air ya kwanta dama yana da shekaru sittin da biyar a duniya, ya rasu ne ranar 23 ga watan Dismaban shekarar 2022
Pele
Sharraren dan wasan kwallon kafan nan na duniya wanda ya lashe kofin duniya har sau uku, Pele, ya rasa ranar Alhamis din nan data gabata yana da shekaru 82 a duniya. .
Asali: Legit.ng