Yara Sun Ga Bature Ido da Ido a Karon Farko, Sun Shiga Mamakin Kyawun Jikinsa
- Wani bature ya nunawa mutane yadda yara kanana bakaken fata ‘yan uwansa suka shiga mamakin ganin fatar jikinsa
- Da suke tambayarsa, yaran sun nemi sanin dalilin da yasa idanunsa da fatarsa suka bambanta da nasu
- Mutane da yawa sun yi martani kan bidiyon, suka ce kawai yaran suna mamakin bambancin halitta ne
Wani bature, @jnpswirl da ke auren wata mata bakar fata ya yada wani gajeren bidiyo da ke nuna yadda ganawarsa da wasu yara danginsa, sun shiga mamakin bambancin fatan jikinsu.
Baturen ya ce, wannan ne karon farko da ya ziyarci nahiyar Afrika, kuma tabbas yana jin dadin ziyarar.
Yaran da ya gana dasu, sun zagaye shi, suna mamakin kamanninsa mai ban mamaki ba irin nasu ba.
Daya daga cikin yaran a cikin bidiyon ta tambayi baturen me yasa yake da hasken fata.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yayin da yaran suka taba jikinsa, sun shiga mamakin laushi da kyawunsa. Daga nan suka fara duba gashin kansa suna tabawa.
Kalli bidiyon:
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, akalla mutane 600 ne suka yi martani a kai, mutum 50,000 sun yi dangwalen nuna sha’awa.
Martanin jama’a
Ga kadan daga abubuwan da mutane ke cewa game da bidiyon:
Jim Bob:
"Sunul ikinsa, wannan yabon kadai zai shajja’a ni na watanni.”
Kelechi Achinike:
"Akwai lokacin da yara suka yi min haka lokacin da na zauna a Vietnam... Yara suna son sanin abu, ba su da nufin cutarwa.”
sosovanny:
"Sumul yake, kai yarinya ta ji wannan abu.”
John Pastor:
"An yi min irin haka a lokacin na ziyarci Kenya da farko kuma gashi ina da zane a jiki.”
iluvgenia<3:
"Wadannan yaran basu da rariya a bakinsu.”
mebble70:
"Yaron na tambaya game da tsinin hancinsa mai kyau.”
Kyakkayawar Budurwa ’Yar Arewa Ta Girgiza Intanet da Yadda Ta Kware a Buga Kwallon Kafa
Ba maza kadai suka kware wajen taka leda ba, mata da yawa sun iya buga kwallo fiye da yadda ake tsammani, inji masu yin wasan.
Wani bidiyo ya nuna lokacin da wata yarinya ke buga kwallo cikin salo mai daukar hankali, mutanen kafar sada zumunta sun yi mamaki.
Da yawan jama'a sun yi martani, wasu sun ce ta fi maza da yawa iya wasa da kwallo musannan ganin yadda ta kware.
Asali: Legit.ng