Malamin Addini Ya Amsa Bukatar Fasto Adeboye Na Neman a Bashi Damar Yin Wa’azi a Masallaci
- Wani shahararren malamin Islama kuma mai wa'azi a ACADIP, Mallam Yusuf Adepoju, ya amshi kalubale daga Fasto Enoch Adeboye na cocin RCCG
- An gano Adeboye a wani bidiyo da ya yadu yana cewa yana duba ga Limaman musulunci su bashi damar yin wa'azi a masallatai a ranar Lahadi
- A martaninsa ga bidiyon, Adepoju ya ce zai ba Daddy G.O dama, yana mai cewa shima zai so yin wa'azi a cocin RCCG a ranar Juma'a
Mallam Yusuf Olatunde Adepoju, babban malami na kungiyar ACADIP ya yarda da kalubalen Fasto Enoch Adeboye, shugaban cocin Redeemed Christian Church of God.
A cewar jaridar Leadership, Adeboye ya yi kira ga Limamai da su bari ya yi amfani da masallatai don yin wa'azi a ranar Lahadi don karfafa hadin kan addini a kasar.
Malamin addinin ya nuna cewa a shirye yake ya tarbi Fasto Adeboye a taronsa na addini yana mai cewa kuma shima zai so yin wa'azi a cocin Redeemed a ranar Juma'a, rahoton New Telegraph.
Halin da ake ciki game da Limamin ACADIP da Faston RCCG
A wani bidiyo da ya yadu, an gano Adeboye yana cewa shi yana duba ga Limaman da za su bari ya yi wa'azi a coci kuma cewa za a ba shugabannin Musulunci damar yin wa'azi a dakin taron RCCG.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Malamin addinin ya fadi haka ne biyo bayan sukar da ya sha kan wa'azi da ya yi a gidan rawa, yana mai cewa bai kai masaukinsa ba.
Malamin ya ce:
"Kamar yadda na bayyana a baya, Ba a hada-hada a gidan rawa a safiyar Lahadi. Masu bacci a gida sune suke yawan zarya a yankin don shan barasa. Saboda haka, wurin yana nan ba kowa ga masu amfaninsa."
A wani labari na daban, dan takarar gwamnan jihar Katsina na jam'iyyar APC a zaben 2023, Dr Umar Dikko ya bayyana cewa zai horar da matasa tare da basu kayan aiki domin murkushe yan bindiga da suka addabi jihar.
Da yake jawabi ga al'ummar Batsari yayin yakin neman zabensa, Dikko ya ce wadannan matasa da za a horar sune za su taimakawa hukumomin tsaro a yaki da suke da miyagu a yankin.
Asali: Legit.ng