Ina Bukatar Mijin Aure, Ban Son Na Mutu Ban Yi Aure Ba: Kyakkyawar Budurwa Ta Koka A Bidiyo

Ina Bukatar Mijin Aure, Ban Son Na Mutu Ban Yi Aure Ba: Kyakkyawar Budurwa Ta Koka A Bidiyo

  • Wata kyakkyawar budurwa Musulma ta bayyana yadda take matukar bukatar namijin aure gaskiya
  • Budurwar ta daura bidiyo a TikTok inda tace ba ta son ta mutu ba ta 'dandana rayuwar aure ba
  • Mabiyanta da jama'ar TikTok sun taimaka mata da addu'an Allah ya bata miji a sabon shekara

Wata budurwa ta daura bidiyo a manhajar TikTok tana kokawa kan yadda har yanzu bata samu mijin aure ba.

A gajeren bidiyon da budurwar mai suna Amrah ta daura, ta bayyana cewa babbar manufarta a rayuwa shine ta wayi gari a dakin mijinta.

A cewarta, zama babu mijin aure babban abin bakin ciki ne,

Amrah
Ina Bukatar Mijin Aure, Ban Son Na Mutu Ban Yi Aure Ba: Kyakkyawar Budurwa Ta Koka A Bidiyo Hoto: TikTok/@baby..amrah
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Amrah ta godewa Allah bisa wayen gari lafiya kuma a matsayin Musulma amma dai tace gaskiyar magana itace mace na bukatar aure.

Kara karanta wannan

Sai Dai Ka Zaba: Budurwa Ta Rabu Da Saurayinta Saboda Mahaifiyarsa Ta Saka Ta Wanke-wanke

Ta ce duk kudin mace a duniyar nan babbar manufarta itace shiga gidan aure.

Ta ce ita dai ta kosa ta shiga gidan miji kuma ta kosa ta sallamawa mijinta kafin ta mutu.

Tace:

"Assalamu Alaikum, gaskiya abin tausayi ne na waye gari sabon wata a gidan miji na ba. Na ji maganganu masu dadi da mara dai akan aure amma nima ina son ayi da ni, ina son sallawa mijina."
"Amma dai na godewa Allah da ya tashe da lafiya kuma Musulma. Maganar gaskiya shine rashin aure ga mace abin bakin ciki ne. Babbar manufar mace shine gidan aure, ku manta da maganganun masu ikirarin yancin mata."
"Gaskiya ban son na mutu ba tare da nayi aure ba."

Kalli bidiyon:

Jama'a sun yi magana kan bidiyon:

Aminu Yusuf KN yace:

"Allah ya azzurtaki da mijin aure nagari abin tunkaho Allahumma Ameen Yarabbil Alameen Oh'Lord, Oh'Lord, Oh'Lord."

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da motoci biyu suka yi karo, mutum 1 ya hallaka, yawa sun jikkata

Shamsu Muhd Abubakar:

"Idan Ta Yarda Bbu Lefe Toh Gobe Nazo A Daura"

Naseer Rabi'u:

"Tazo Mu Rufawa Juna Asiri.. Na Bata Pi Network A Matsayin Sadaki"

Abubakar Umar:

"Allah zabamiki miji nagari me tsoron Allah ameen"

Auwal Bello Abin Godiya:

"Allah yakawo mafita Allah yakawo nagari AMIN Allah yakarawa shugabamu fiyayen halita anabbi muhmmaduh rasulilahin s a w daraja AMIN"

Abubakar Umar yace:

Allah zabamiki miji nagari me tsoron Allah ameen

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida