AbdulJabbar: Yan Shi'a Sun Kai Karar Gwamnatin Kano Wajen Majalisar Dinkin Duniya

AbdulJabbar: Yan Shi'a Sun Kai Karar Gwamnatin Kano Wajen Majalisar Dinkin Duniya

  • Kungiyar yan Shi'a sun shigar da gwamnatin jihar Kano kara wajen kungiyoyin kasashen duniya
  • Yan Shi'a sun ce hassada ce Malaman da suka yi zaman titsiye suka yiwa Abduljabbar saboda binciken da yake yi
  • Hakazalika sun ce ra'ayoyin da ya bayyana kan bidiyon Gandollar na cikin dalilan da yasa ake masa bita da kulli

Abuja - Kungiyar mabiyar akidar Shi'a a Najeriya watau Islamic Movement in Nigeria (IMN), ta bukaci a gaggauta sakin Sheikh Abduljabbar Kabara, da kotu ta yankewa hukuncin kisa.

Zaku tuna Legit ta rahoto muku yadda babbar kotun Shari'a dake jihar Kano karkashin jagorancin, Alkali Sarki Yola, ta yankewa Abduljabbar Kabara, hukunci kan batanci ga Manzon Allah (SAW).

Kungiyar IMN ta ce laifukan da aka tuhumi AbdulJabbar Kabara da su da kuma hukuncin matsayin sharri kuma da siyasa ciki, rahoton SR.

Kara karanta wannan

Kudin Da Aka Sace Karkashin Buhari Idan Aka Rabawa Yan Najeriya Kowa Zai Samu N700,000

AbdulJabbar
AbdulJabbar: Yan Shi'a Sun Kai Karar Gwamnatin Kano Wajen Majalisar Dinkin Duniya
Asali: UGC

A ranar Laraba a Abuja, kungiyar IMN ta hannun kungiyar dalibanta ta shigar da kara wajen majalisar dinkin duniya (UN), gamayyar kasashen Turai (EU), hukumar kare hakkin dan Adam a Najeriya, majalisar lauyoyi, Amnesty International da kuma Human Right Monitor.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A wasikar, kungiyar ta bukaci a dau matakin gaggawa kan gwamnan Kano da kotun shari'ar Musulunci su sake nazari kafin zartar da wannan hukunci.

Wasikar ta sake kira ga a daukaka kara domin watsi da hukuncin Alkali Ibrahim Sarki Yola.

A cewar takardar:

"Muna wannan rubutu ne domin janyo hankalinku bisa hukuncin karya da akayi na yankewa Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara na kisa a jihar Kano ta hanyar rataya; kuma muna kira ga al'umma su kawo masa dauki har a sake shi."
"Sheikh Abduljabbar babban malami ne kuma 'dan Sheikh Nasuru Kabara Kano. Iyalan Sheikh Nasuru Kabara Kano mutane ne da ake girmamawa ba a Najeriya kadai ko Afrika ba, har a fadin duniya."

Kara karanta wannan

Saura kwanaki 20: Gwamnatin Kano ta aiwatar da umurnin kotu kan Abduljabbar, saura na kisa

"Kwanakin nan, wadanda suka saurari jawaban wasu dakewa kansu ikirarin Malaman Musulunci a jihar Kano da wasu jihohin Najeriya sun shaida yadda hassada tsakanin Sheikh Abduljabbar da Malaman bisa sabbin binciken da yake gudanarwa."
"Bugu da kari, faifan odiyo da bidiyon da ana iya gani a fili hujja ne ga cewa Malaman da ke da banbancin ra'ayi da Sheikh AbdulJabbar suka tarun masa kawai don su hana shi yada Ilimi."
"Hakazalika, ra'ayoyin Sheikh AbdulJabbar kan bidiyon Gandollar da jaridar DailyNigerian ta wallafa ya taka rawar gani wajen tada rikici tsaknin Malamin da Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje."

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida