San Kirsimeti Ya Halaka Shugaban Matasa a Jihar Bayelsa
- Yayin da ake shirye-shiryen bikin kirsimeti, farin ciki ya karade al'umma wanda haka yasa mutane da dama yanka dabbobi don gudanar da bikin
- Sai dai, wani shugaban matasan yankin Obogoro na karamar hukumar Bayelsa ya rasa ransa dalilin wata saniya da ta aikasa lahira
- An ruwaito yadda mahauta biyun da aka gayyata don yanka saniyar suka kasa tsaida ta don daure mata kafafuwa, daga bisani ta farwa matashin gami da tumurmusarsa
Bayelsa - Wani abun tashin hankali ya auku a anguwar Obigoro cikin karamar hukumar Yenagoa na jihar Bayelsa yayin da saniyar bikin kirsimeti ta halaka wani shugaban matasan yankin, Mista Sobokime Igodo.
Daily Trust ta tattaro yadda marigayin da gungun abokansa suka hada kudi suka siya saniya don su raba kamar yadda suka saba a kowacce kirsimeti.
Kamar yadda mazauna yankin suka bayyana, lamarin ya auku ne a gidan marigayin inda ya kamata a yi kakkawar saniyar.
An gano yadda mahauta biyun da aka gayyato don su yanka saniyar suka kasa tsaida saniyar don su daure mata kafa kafin yanka ta.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sai dai, Igodo yana kan amsa kiran waya kafin daga bisani saniyar ta auka masa tare da tumurmusarsa, gami da hambarinsa tare da maka gadon bayansa a kasa.
An gano yadda aka garzaya da shi cibiyar asibitin tarayya (FMC), Yenogoa inda daga nan aka maida shi asibitin koyarwa na Port Harcourt.
Wata majiya ta tabbatar da yadda shugaban matasan daga baya ya mutu a asibitin koyarwa na Port Harcourt.
Yayin da aka tuntubi kakakin 'yan sandan jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, ya musanta sanin aukuwar lamarin.
Sai dai yayi alkawarin tuntubar shugaban 'yan sandan yankin sannan ya sanarwa wakilin Daily Trust.
Da Kaina na Ja Masa: Budurwa Ta Tafkawa Tsohon Saurayinta Asiri da Jininta Kan Kin Karbar Cikin da Yayi Mata
Malamai da matasa sun ziyarci Kirista a coci a Zaria
A wani labari na daban, matasa da malamai mabiya addinin Musulunci sun ziyarci wata majami'a dake Samaru a garin Zaria.
Sun taya Kirista bikin Kirsimeti tare da kai musu kyautuka inda suka nemi hadin kan juna don zaman lafiya a kasar nan.
An ji yaddda Musulman suka zage tare da dibar garar Kirsimetin duk don kulla alaka mai kyau da mabiya addinin Kiristan a ranar Lahadi da ta gabata.
Asali: Legit.ng