Ku Yi Mun Biyayya da PDP Ko Na Tsige Ku, Gwamna Mohammed Ga Masu Rike Da Mukamai
- Gwamna Bala Mohammed na Bauchi ya yi kakkausan gargadi ga masu rike da mukaman siyasa a jihar
- Mohammed ya yi barazanar tsige duk jami'in da ya samu da rashin biyayya ga gwamnatinsa da jam'iyyar PDP
- Ya fadi hakan ne yayin rantsar da sabbin kwamishinoni biyu da wasu da aka baiwa mukamai a gwamnatin jihar
Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yi barazanar sallamar duk wani mai rike da mukami da aka kama yana rashin biyayya ga gwamnatinsa da jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Gwamnan ya yi gargadin ne a yayin rantsar da sabbin kwamishinoni biyu, mai basa shawara daya da kuma shugabannin rikon kwarya na kananan hukumomi 20 a karshen mako a Bauchi, Daily Trust ta rahoto.
Ya ce:
"Bari na gargadi daukacin sabbin mutanen da aka baiwa mukamai cewa gwamnatin nan bata da gurbi ga jami'ai masu rashawa, rashin biyayya da rashin gogewa. Ku zamo masu biyayya ga gwamnati mai ci a jihar nan sannan ku jajirce a kan manufofinta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Don kore shakku, bari na fito fili na bayyana cewa ba zan yi kasa a gwiwa ba wajen tsige duk jami'in da aka samu da rashin biyayya ga gwamnatin ko jam'iyyarmu mai albarka ta PDP."
An maye gurbin kwamishinoni 2 da suka bar majalisar zartarwar Bauchi da wasu
Mohammed ya yi bayanin cewa nadin sabbin kwamishinonin biyu ya biyo bayan ficewar Dr Aliyu Usman Tilde, tsohon kwamishinan ilimi da Hon Abdullahi T. Musa, tsohon kwamishinan raya kakkara da ayyuka na musamman daga majalisar zartarwa na jihar.
Ya ce Dr Tilde ya yi murabus ne don ra'ayin kansa yayin da Musa ya bar majalisar zartarwa na jihar don nada shi a wani matsayi.
Jaridar Daily Trust ta nakalto gwamnan yana cewa:
"Saboda haka, an cike gurbin da tsoffin kwamishinonin suka bari da Malama Jamila Mohammed Dahiru da Hon. Amina Mohammed Katagum don maye gurbin Dr Aliyu Tilde da Hon Abdullahi Musa."
Rikicin PDP na Iya Zama Babbar Barazana ga Atiku a Jihar Kano
A wani labarin kuma, hasashe sun nuna cewa zai yi matukar wahala dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya kawo kuri'un Kano a zaben 2023.
Hakan ya biyo bayan tabbatar da Mohammed Abacha da wata babbar kotun tarayya ta yi a matsayin sahihin dan takarar gwamna.
Asali: Legit.ng