Kudin Da Aka Sace Karkashin Buhari Idan Aka Rabawa Yan Najeriya Kowa Zai Samu N700,000

Kudin Da Aka Sace Karkashin Buhari Idan Aka Rabawa Yan Najeriya Kowa Zai Samu N700,000

  • Babbar jami'ar gwamnatin Buhari ta bayyana cewa kudin da aka wawura karkashin gwamnatin nan ba kadan bane
  • Hajiya Naja'atu ta kasance yar gwagwarmaya kuma yar siyasa tun lokacin da Buhari ke jam'iyyar adawa
  • Shugaba Buhari ya hau mulki ne bisa alkawarin yaki da rashawa tare da dakile matsalar rashin tsaro

Kano - Kwamishana a hukumar jin dadin yan sanda PSC, Naja'atu Mohammed, ta bayyana cewa kudaden da ma'aikatan gwamnati suka sace cikin shekaru 8 da suka shude ba kadan bane.

A cewarta, da za'a rabawa kowani dan Najeriya wadannan kudade, kowa ya samu N732,000.

Ta bayyana hakan ne ga ahirar da tayi Freedom FM, Kano yayin taron gabatar da lambar yabo ga wani jami'in dan sanda, Daniel Iste Amah.

Cibiyar wayar da kai kan adalci da gaskiya watau Center for Awareness on Justice and Accountability, CAJA tare da hadin kan Penlight Center for New Media Innovation.

Kara karanta wannan

CBN Ya Bayyana Makudan Kudin Da Aka Kashe Wajen Buga Sabbin Naira Da Lalata Tsaffi

Naja'atu
Kudin Da Aka Sace Karkashin Buhari Idan Aka Rabawa Yan Najeriya Kowa Zai Samu N700,000
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwanakin baya, Legit Hausa ta kawo muku rahoton jami'in dan sandan da shugaba Buhari ya karrama kan kwatanta gaskiya da tsoron Allah inda ya ki karban cin hancin $200,000 daga wajen wani barawo a Afrilun 2022.

Hajiya Naja'atu ta bayyana cewa idan ba dakile wannan satan da ake yi ba, nan da 2030 kudin da za'a sata zai kai a rabawa kowani dan Najeriya N1.4m, rahoton DailyNigerian.

Tace:

"Daga 2014 kawo yanzu, kudin da aka sata a Najeriya na da yawa. Da za'a rabawa kowani dan kasa, har da jaririn da aka haifa yau, sai kowa ya samu N732,000."
"Bisa bincike, idan kuma aka cigaba da hakan har nan da 2030, abun zai munana. Idan za'a dawo da dukkan kudin da aka sata a lokaci, sai kowa ya samu N1.4million matsayin rabonsa."

Kara karanta wannan

Manyan 'Barayi' da 'Macuta' Al'umma 4 Da Asirinsu Ya Tonu a 2022

"Babban kalubalen kasar nan shine cin hanci da rashawa. Sune tushen kowani matsala da kasar nan ke fuskanta."

Na yiwa Najeriya iyakan kokari na

Shugaba Buhari a makon da ya gabata ya cika shekaru 80 a duniya.

Manyan hadimansa da Ministocinsa sun shirya masa liyafa ta musamman domin murnar wannan rana.

Buhari ya bayyana musu cewa shi fa ya yiwa Najeriya iyakan kokarinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida