Kar Ka Batawa Kanka Lokaci Wajen Yiwa Tinubu Kamfen Jam'iyyar PDP Ga Buhari

Kar Ka Batawa Kanka Lokaci Wajen Yiwa Tinubu Kamfen Jam'iyyar PDP Ga Buhari

  • Shugaba Buhari ya nuna karara cewa yana tare da dan takarar jam'iyyar APC bola Ahmed Tinubu Kuma zai Goya Masa Baya 100 bisa 100
  • A wata ziyara da tinubu ya kaiwa Buhari an jiyo shugaban na cewa jam;iyyar APC ce zata lashe dukk kujerun zaben a 2023
  • Mataimakin shugaban kasa Prof. Yemi Osinbajo ya kaiwa dan takara shugaba kasa na jam;iyyar APC ziyara a gidansa a Abuja

Abuja: Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar PDP yace bai kamata ace shugaban Buhari yace zai batawa kansa lokaci ba wajen yiwa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC yakin kamfe ba, domin batawa kansa lokaci ne.

PD-APC
Kar Ka Batawa Kanka Lokaci Wajen Yiwa Tinubu Kamfen Jam'iyyar PDP Ga Buhari Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben, Kola Ologbondiyan ne yayi wannan kiran a Abuja, yace yan Nigeria sun riga sunyi tutsun jaki ga dan takarar APC, Tinubu, suna masu bayyana cewa ba ruwansu da wanda ya wawushi dukiyar kasa ko kuma yai wa kasa illa ba

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Buhari Ya Bayyana Adadin Kujerun Da Jam'iyyar APC Za Ta Lashe

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa sanarwa tace

"Karara yake bayyane a fuskokin 'yan NIgeria kan rashin amincewarsu ko yarda ga dan takarar da cin hanci da rashawa ya mamaye, gazawa, rashin usuli, zargin ta'ammali da miyagun kwayoyi, suna cike da ayoyin tambaya kan yarda dan takarar yake, shi kana ganin zasu amince masa"
"Ina mai tabbatar maka da cewa 'yan Nigeria baza su yarda Nigeria ta koma halin da wadannan ko dai-daikun suka jefata a ciki. Wadannan mutanen sun riga sun lalata yanayin kasa a idanun duniya da ma ko ina da kake tunani."

Thisday ta rawaito cewa Ologbodiyan yace:

"Irin wadannn abubuwan karyar da dan takarar shugaban kasa yake fada bazasu wani tasiri akan yan kasa ba, ya fada mana wani abu wanda yayi a matsayinsa na gwamnan jihar Lagos wanda zuwa yanzu za'a amfana. Amma bashi da aiki sai karyar yayi kaza da kaza."

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Atiku Ya Bayyana Abinda Zai yi Idan Ya Sake Fadi Zaben Shugaban Kasa

"Ba dan Nigeria dan zai sake zaben wannan gwamnatin da ta gaza a kowanne fanne"

Ina Ba'a Zabi Tinubu Ba Wa Ya Kamata A Zaba

A halin yanzu, kai maganar da ana ke maka yan Nigeria sun yanke shawarar zabar dan takarar jama'iyyar PDP. Alhaji Atiku Abubakar, sabida sanin shine zai kada Tinubu kuma shine zaai kawowa kasa sauyi.

Ologbondiayn yace yana da tabbaci kan Atiku wajen tafikar da gwamnati, juriya, rikon amana da kuma sanin ya kamata wajen tafiyar da al'umma dama kasa baki daya, dan haka ba wanda ya cancanci ya mulki kasar nan sama da Atiku Abubakar.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida