Ba Zan Zuba Ido Ina Gani 'Yan Ta'adda Na Kashe Mutanen Jihata Ba, Ortom
- Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, yace gwamnatinsa ba zata tsaya tana kallo wasu miyagu na kashe al'umma ba
- Ortom ya raba Motocin sintiri guda 25 da kuma Babura sama da 700 ga jami'an tsaron da gwamnatinsa ta kafa
- Yace hare-haren mayaƙan da ake zargin Fulani makiyaya ne ya kai gwamnatinsa bango, zata yi duk mai yuwuwa
Benue - Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, yace gwamnatinsa ba zata sake rungume hannu ta bari ana kashe mutane tamkar dabbobi ba.
Jaridar Tribune fa rahoto cewa gwamnan ya faɗi haka ne a wurin miƙa sabbin motocin aiki ga jami'an sa'kai (BSCVG) na jihar Benuwai da gwamnatinsa ta kirkira.
Da yake jawabi a wurin, gwamna Ortom ya jaddada cewa gwamnatinsa zata ci gaba da yaƙar Fulani makiya waɗanda ake zargin su ke kai hare-hare a jihar.
Ya ce hare-haren ta'addancin mayaƙan Fulani makiyaya kan mutanen ba su ji ba basu gani ba ya kai jihar Benuwai bango, ba zai yuwu haka ta cigaba ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A kalamansa gwamna Ortom ya ce:
"Ba zamu cigaba da zama mu zuba ido mu bari ana kashe mana mutane ba, a halin yanzu an kai mu bango, zamu jawo dukkan mazajenmu don kare kanmu daga kisa."
Haka zalika yace yana jiran amincewar shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne kan bukatarsa ta sayo bindigun AK47 a raba wa dakarun tsaro na jihar Benuwai.
Bayan haka gwamnan ya damƙa sabbin motoci ga Jami'an dake tsare dabbobi domin su samu damar kewaye ko ina su tabbatar da dokar hana kiwo a fili.
Jumullan motoci tsaro 25, Mashina 769 gwamnatin Benuwai karkashin Ortom ta sayo kuma ta raba wa rundunonin guda biyu da ta samar.
Dakarun BSCVG sun samu Motocin aikin tsaro 23 da Babura 460. Yayin da jami'an yaki da kiwon Fili suka samu Motoci biyu da Babura 30.
Bugu da ƙari an raba wa Sarakunan grgajiya musamman Dagatai Babura domin su samu damar kula da yankunansu yanda ya kamata.
Daga karshe gwamna Ortom ya yaba wa rundunar Operation Whirl Stroke, OPWS, Cibil Difens da sauransu bisa gudummuwar da suka bayar wa na gina ƙasa mai zaman lafiya.
Ku Zabi Mutum Nagari Ba Wai Jam'iyya Ba, Gwamna Ortom Ga Yan Najeriya
A wani labarin kuma Gwamna Ortom ya shawarci mutanen Benuwai su yi nazari sosai kan mutanen da zasu zaɓa a 2023
Da yake jawabi bayan sa hannun a kasafin kuɗin 2023, gwamnan na jam'iyyar PDP ya roki mazauna su zabi cancanta ba jam'iyya ba
Ortom na ɗaya daga cikin gwamnonin tawagar gaskiya watau G5 waɗanda ke adawa da shugaban jam'iyar PDP na kasa.
Asali: Legit.ng