Wata Babba Motar Kwantena Ta Fadi Kan Motoci, Wani Direba Ya Mutu, Jama’a da Yawa Sun Jikkata a Legas

Wata Babba Motar Kwantena Ta Fadi Kan Motoci, Wani Direba Ya Mutu, Jama’a da Yawa Sun Jikkata a Legas

  • Wani mummunan yanayi ya faru a jihar Legas yayin da wata babbar mota kwantena ta fadi a kusa da tashar bas ta Cele
  • Wannan lamari ya kai ga mutuwar diraban motar kasuwanci, kana wasu mutane da yawa sun jikkata
  • Ya zuwa yanzu dai an dauko motar daga nauyi domin kokarin dage motar da ke kwance kan motoci a bakin hanya

Apapa, jihar Legas - Wani bidiyon da jaridar Vanguard ta yada ya nuna lokacin da wata babbar mota kwantena ke kwance kan wasu kananan motoci a gefen a hanya a wani yankin jihar Legas.

Wannan lamari dai ya faru ne ranar Alhamis 22 ga watan Disamba a tashar bas ta Cele da ke kan babban titin Oshodi Apapa a jihar, kamar yadda bidiyon ya bayyana.

Kara karanta wannan

Budurwar ta Koma Tukin Mota Bayan Sana'ar Koyarwa, Tana Samun N64m Duk Shekara

Kamar yadda wakilin Legit.ng Hausa ya gani, motar ta komade ga kuma wasu motoci da ke karkashinta.

Rahoton ya ce, motoci uku ne kwantenar mai girman kafa 40 ta danne, kuma a yanzu haka ana ta kokarin yadda za a cire su.

Mota ta fadi a Legas
Wata Babba Motar Kwantena Ta Fadi Kan Motoci, Wani Direba Ya Mutu, Jama’a da Yawa Sun Jikkata a Legas | Vanguard News
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ana fargabar mutane da yawa sun mutu a yayin wannan mummunan hadarin da aka ce direban wata mota ya mutu.

Mutane da yawa sun raunata

Hakazalika, rahotannin da muke samu sun bayyana cewa, akwai mutane da yawa da suka samu raunuka, har yanzu ana ci gaba da aikin ceto.

A bidiyon, an ga lokacin da motar daga kayan nauyi ta zo domin kokarin dage babban motar kana da ceto kananan motocin da ke kasanta.

A bangare guda, mutane da yawa sun yi carko-carko don game ma idanunsu abin da ke faruwa da kuma yiwuwar ba da agaji a inda ba a rasa ba.

Kara karanta wannan

Aiki ya jika: Bayan kowa ya yi ankon N150k, amarya ta fece, ango da abokansa sun girgiza

Hakazalika, bidiyon ya nuna hayaniyar jama'ar da ke gefe, lamarin da yasa jami'an tsaro ke ta kokari shawo kai da kwantar da hankalin jama'a.

Kalli bidiyon:

Rayukan Mata da Kananan Yara 11 Sun Salwanta a Hatsarin Mota

A wani labarin kuma, hadarin mota ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 11 a hanyar Kano zuwa Zaria a Arewacin Najeriya.

Wannan lamarin ya faru ne a ranar Asabar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ana yawan samun hadurran mota a Najeriya, hukumomin tsaro, agaji da kare haddura na aikin ceto jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.