Wakiliyar Gwamnan Babban Bankin Najeriya ta Gurfana Gaban Majalisa
- Aisha Ahmad, Mataimakiyar gwamnan babban bankin Najeriya a halin yanzu tana gaban majalisar wakilan Najeriya inda take kora jawabi
- Har sau biyu gwamnan babban bankin aka aike masa da goron gayyata daga majalisar amma ya kasa halarta saboda rashin lafiya
- Ahmad ta sanar da cewa da yawan hada-hadar kudaden na jama’a da kamfanoni kashi 92 da 82 sun koma na turawa ba a tsaba ba
FCT, Abuja - Mataimakiyar Gwamnan babban bankin Najeriya, Aisha Ahmad a yanzu tana jawabi ga majalisar wakilan Najeriya kan dokokin su na kwanan nan wanda daga ciki aka kayyade yawan kudin da za a dinga cirewa a bankuna.
Majalisar tayi kiran gaggawa ga Gwamnan bankin, Godwin Emefiele, wanda ya ki zuwa gaban ‘yan majalisar har sau biyu.
CBN ta sanar da majalisar cewa Emefiele ba zai bayyana gaban majalisar ba amma Ahmad zata jagoranci kwamitin gwamnonin zuwa gaban ‘yan majalisar.
Kamar yadda Ahmad tace, CBN ta gano cewa kusan kashi 94 da kashi 82 na hada-hadar kasuwanci duk ana yin su ne ta hanyar tura kudi wanda hakan ke nuna cewa wannan adadin da aka saka ba zai wani shafi jama’a ba.
Mataimakin shugaban bankin ta sanar da ‘yan majalisar cewa babban bankin ya kawo tsarikan ne kashi-kashi wanda aka fara samun nasarorinsu a wasu jihohi da aka fara kaddamarwa.
Karin bayani na nan tafe…
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng