Munyi Dana Sanin Abinda Sojijin Mu Suka Aikata A Jihar Zamfara

Munyi Dana Sanin Abinda Sojijin Mu Suka Aikata A Jihar Zamfara

  • A wannan makon ne sojoji sukai lugudan wuta a jihar Zamfara akan 'yan bindiga, wanda kuma ya shafi fararen hula
  • Akalla an kiyasta mutum 69 da suka rasa ransu baya da kuma wasu da dama suka jikkata dalilin harin
  • Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya tabbatar da faruwar al'amarin a yankin Matunji da ke jihar

Abuja: Gwamnatin tarayya ta nuna bakin cikinta da damuwarta kan rasa rayuka da aka samu a karamar hukumar mulki ta maru, bisa wani hari da sojojin kasar nan suka kai a jirgi.

Daga cikin wadanda abin ya shafa akwai yaran kauyuka da dama wanda suke kewaye da juna da suka rasa ransu sabida kai harin.

Tun da fari dakarun sojin sunce su auna iya inda ''yan bindigar suke, amma daga bisani 'yan bindigar suka shiga cikin kauyukan.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Daure Matar Wani Dan Majalissa Kan Yunkurin Kasheshi Ta Mallake Dukiyarsa

Lai Muhammad
Munyi Dana Sanin Abinda Sojijin Mu Suka Aikata A Jihar Zamfara Hoto: Vanguard
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da yake magana kan batun tun da fari, Gwamna Bello matawalle yace:

"Yan bindiga da dama sun rasa ransu, a wannan karshen makon da muka wuce, duk da har yanzu bamu samu labarin rayuka ko asarar dukiya da fararen hula suka yi ba"

Yayin zantawarsa da jaridu ciki harda wakilin jaridar The cable, ministan labarai da al'adu Lai Muhammad yace gwamnati ta dau alhakin wannan abun.

"Bisa ga wannan abun da ya faru na rasa rayuka da dama a jihar Zamfara, Ina mai sanar muku da gwamnatin tarayya tana jimami tare da nadamar kai harin."
"Kokarin yakin ta'addanci ko rashin tsaro abu ne mai wahala, duk da muna sane da yadda sojojin sama ke lura sosai yayin gudanar da aiyukansu, Amma bisa wannan rashin muna dana sani kan hakan

Kara karanta wannan

Gwamna Matawalle Ya Faɗi Gaskiyar Abinda Ya Faru Har Jirgin Soji Ya Kashe Mutane a Zamfara

Ana Samun Irin Haka

Lai Muhammad Ya Ci gaba da cewa yanayin yaki ne haka, duk da yadda sojoji suke kula dole ne za'a samu sabani, musamman ma tunda niyyarsu itace kawo karshen wannan matsalar tsaron data damu kowa.

Jaridar The Sun ta rawaito cewa hukumomin sojin sama ma sun bada hakuri kan wannan abinda ya faru, suna cewa sun aikata ne bisa rashin sani ko ajizanci na dan adam da ba makawa watara sai ya hadu dashi ko kuma ya aikatashi bai sani ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida