Ban Tunanin Zan Sake Takara Zabe Idan Na Fadi Wannan, Atiku
- Dan takaran kujerar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce ya dade yana son zama shugaban kasan Najeriya
- Atiku Abubakar babbar manufarsa a rayuwa yanzu shine ya shugabanci kasar nan muddin yana da karfi da lafiya
- Amma dai dan siyasan ya bayyana cewa da yiwuwan zaben 2023 ya zama na karshen da zai yi
- Wani hadimin tsohon mataimakin shugaban kasan ya zayyana yadda Atiku zai kada Tinubu a zaben 2023
Lagos, Nigeria - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi takaran kujeran shugaban kasa sau biyar a rayuwarsa.
Yanzu yana takararsa na shida a 2023 don gaje kujerar shugaba Muhammadu Buhari.
A wani hira da mujallar Financial Times ta wallafa, Atiku ya ce zai cigaba da takarar kujerar shugaban kasa muddin yana cikin raye kuma cikin koshin lafiya.
Financial Times ta ruwaitosa da cewa:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Manufata ce ta rayuwa cewa muddin ina raye kuma da lafiya, zan cigaba da cimma manufar."
Tace ya bayyana hakan ne ranar yakin neman zaben PDP da ya gudana a Legas.
Na kai makura, Atiku
Bayan cewa zai cigaba da takara, Atiku ya bayyana cewa da yiwuwan wannan ya zama na karshe.
A cewarsa:
"Na kai muntaha. Ban tunanin zan sake takara bayan wannan."
Yadda Atiku zai lashe zaben 2023
Wani babban hadimin dan takaran shugaban kasan PDP wanda mujallar FT ta sakaye sunansa ya bayyana yadda maigidansa zai lashe zaben 2023.
Hadimin ya ce zai kara da Bola Tinubu na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da Peter Obi na jam'iyyar Labour Party LP a kudu sannan kuma ya lallasasu a Arewacin Najeriya.
Babban Jigon Jam'iyyar Adawa ta PDP a Ibadan Ya mutu Bayan Shekaru 62 a Duniya
A wani labarin kuwa, babban jigo kuma tsohon magatakardan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Oyo, Hanarabul Taofeek Olayiwola, ya kwanta dama.
A ruwaito cewa Taofeek Olayiwola ya rasu ne a a Asibitin jami'ar Ibadan, babbar birnin jihar.
Mamacin ya kasance Sakataren jam'iyyar PDP ne a zamanin mulkin tsohon gwamnan Oyo, Gwamna Adebayo Alao-Akala wanda shima ya mutu a bara.
Gwamnatin jihar Oyo, tare da yan uwa da abokan arziki sun aika sakonnin ta'aziyyarsi.
Asali: Legit.ng