Gwamnan Babban Bankin Najeriya Ba Shi da Lafiya, Ba Zai Je Majalisa Ba

Gwamnan Babban Bankin Najeriya Ba Shi da Lafiya, Ba Zai Je Majalisa Ba

  • Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya kwanta rashin lafiya ba zai samu zuwa kiran majalisa ba inji mataimakinsa
  • Sai dai maimakon haka, Edward Adamu, yace gwamnan zai tura mataimakiyarsa ta wakilce shi ranar Alhamis
  • Duk da Alla wadai da sukar da ake masu, majalisar wakilan tarayya ta kafe dole sai CBN ya janye sabon tsarin da ya bullo da shi

Abuja - Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ba zai samu zuwa gaban majalisar wakilan tarayya ba a ranar Alhamis, a cewar CBN.

Maimakon haka, mataimkiyar gwamnan CBN a bangaren tsarin daidaita kuɗi, Aisha Ahmad, ce zata wakilce shi wajen amsa gayyatar majalisa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Godwin Emefiele.
Gwamnan Babban Bankin Najeriya Ba Shi da Lafiya, Ba Zai Je Majalisa Ba Hoto: punchng
Asali: UGC

A wasikar baya bayan nan da mataimakin gwamnan CBN na bangaren harkokin haɗaka, Edward Adamu, ya aike wa majalisar wakilan, yace Godwin Emefiele na fama da rashin lafiya.

Kara karanta wannan

Da Dumi-ɗumi: Shugaba Buhari Ya Gana da Kakakin Majalisar Wakilai Kan Muhimman Abu 2

Ya ce sakamakon wannan rashin lafiya gwamnan ba zai samu halarta da kansa ba amma zai tura wakili.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa a ranar Talata 20 ga watan Disamba, 2022 Emefiele ya gaza amsa kiran mambobin majalisa a karo na biyu.

Duk da sukar da suke sha da Allah wadai, 'yan majalisar wakilan sun sake tsara zuwan gwamnan CBN gabansu ranar Alhamis, sun jaddada kudirinsu na ganin bankin ya janye sabon tsarin kayyade cire kuɗi.

Majalisa ta aika wa Emefiele da sammaci ne domin ya zo ya masu ƙarin haske kan sabon tsarin, wanda ya kayyade adadin kuɗin da mutum zai iya cirewa a banki duk mako.

Shin majalisar ta amince gwamnan CBN ya tura wakili?

Bayan Femi Gbajabiamila, shugaban majalisa ya karanta wasikar Amadu ga mambobi a tsakiyar zamansu na yau Laraba, yan majalisun sun amince da wakilcin gwamnan babban bankin.

Kara karanta wannan

Da Dumi-dumi: Gwamnan CBN Ya Sake Kin Bayyana a Gaban Majalisa Karo Na Biyu, Yan Majalisa Sun Yi Martani

A wani labarin kuma Shugaba Buhari ya gana da kakakin majalisar wakilan tarayya kan batun sabon tsarin CBN

A zaman shugabannin biyu sun tattauna kan batun kayyade kuɗin da mutum zai iya cirewa kullum daba banki yadda babban bankin ya bullo da shi.

Hakanan Femi Gabajabimila ya ce sun kuma taɓo abubuwa da dama da ya haɗa da batutuwa da suka danganci babban zaɓen 2023 mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262