An Maidowa Da Nigeria Kudin Ciyar Da Alhazai Da Ya Gaza Sabida Wasu Matsal-tsalu
- Sakamakon gazawar ciyar da alhazan Nigeria abinci mai kyau ko kuma karancinsa, an dawowa da hukumaralhazan Nigeria N107m
- A ranar talatan nan hukumar alhazan Nigeria, ta bakin shugaban hukumar alhgazan ta kasa yace Saudi Arabia ta dawowa da Nigeria kudin abincinta
- A bara alhazan Nigeria sun koka kan yadda suka fuskanci karancin abinci a lokacin aikin hajjin ba, baya ga matsaltsalun da wasu maniyata suka samu na rashin zuwa kasar
Abuja: Hukumar Kula da alhazan Nigeria NAHCON, tace ta samu Riyal 542,033 daidai da N107,864,567 sabida kasa ciyar da alhazan Nigeria a hajjin da aka gudanar a wannan shekarar.
Wani kamfani mai suna Mutawwwif wanda ke kasar Saudi Arabia, sune suke da alhakin ciyar da alhazan Nigeria abinci da zriga-zirga da kuma muhallin da zasu sauka.
Dawo da kudin ya faru ne sakamakon gazawar kamfanin na yin abinda ya kamata dan gane da ciyar da alhazan Nigeria. Kamar yadda Daily Trust ta rawaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wata sanarwa da jaridar The Guardian ta samu tace:
"A takardar da shugaban kamfanin ya sanyawa hannu, Dr Ahmed bn Abbas, yace mun gano cewa akwai rarar kudi daga cikin kudin da kuka biya na alhazan ku da kuma sauran wasu bukatu, dan haka muke dawo muku da kudinku dan samun alaqa mai kyau. Dan haka muke dawo muku da wannan kudin, wanda ya kai N107 da doriya."
A bangaren shugaban hukumar NAHCON, yace wannan ba karamin ci gaba bane, kuma yaji dadin da wannan abun, kamar yadda yace da kansu sunyi korafi kan irin abubuwa da suka faru da alhazansu a lokacin aikin hajjin bana
"Nayi mutuqar godewa wannan kamafanin kan wanndan batun da sukayi na dawo mana da gutun kudin alhazan mu"
"Tun lokacin da ake gudanar da aikin mun yi wannan korafin domin ganin an inganta yadda ake ciyar da lhazan mu, kuma sun karbi korafin mu"
Shin Ko Kudin Ya shiga Asusun Hukumar
Yayin da ake tambayar shugaban hukumar, kan ko kudin yazo hannu yace mai magana da yawun hukumar Mousa Ubandawaki ne zai amsa tambayar.
Ubandawaki yace kudin bai shigo aljihun hukumar ba tukunna amma suna jira da tsammanin shugowarsu. .
Abin tambaya anan shine ko shin hukumar zata rabawa hukumomin alhazan jihohi kudin dan su rabawa alhazansu , ko kuma za'ai amfani da kudin dan biyan wasu bukatun hukumar.
Asali: Legit.ng