Hukumar Hisbah Ta Kama Matasa 19 Da ke Kokarin Kulla Auren Jinsi a Jihar Kano
- Jami'an hukumar Hisbah sun cika hannu da wasu matasa 19 a kokarinsu na kulla auren jinsi daya
- Yan Hisbah sun kama mata 15 da maza hudu a wajen daurin auren Mujahid da Abba
- Ainahin wadanda za a daurawa auren sun taere amma an kama uwar bikin mai suna Salma
Kano - Hukumar Hisbah da ke lura tare da tabbatar da da'a tsakanin al'umma ta kama wasu matasa 19 kan halartan bikin auren jinsi daya.
Kakakin hukumar ta Hisbah, Malam Lawan Ibrahim, ya bayyana a ranar Talata, 20 ga watan Disamba, cewa matasan sun hadu ne domin shaida daurin auren wasu da ake zargin yan luwadi ne du biyu, Abba da Mujahid, jaridar Punch ta rahoto.
Wadanda za a yiwa auren sun tsere
Ango da amaryar (Abba da Mujahid) sun gudu a lokacin da jami'an na Hisbah suka isa wajen bikin.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ibrahim ya ce:
"Kamun ya biyo bayan wani bawan Allah ya sanar da hukumar game da auren jinsi daya da ake kokarin hadawa.
"Jami'anmu da ke aiki da hedkwatar hukumar Hisbah, yankin Sharada Kano, sun isa wajen kafin a fara kulla auren.
"Daga cikin wadanda aka kama akwai mata 15 da maza hudu.
"Abba da Mujahid sun tsere jim kadan bayan jami'an Hisbah sun isa wajen daurin auren, amma wacce ta shirya bikin, Slam Usman mai shekaru 21 na a hannunmu.
"Za a mika wadanda aka kama zuwa ga yan sanda don daukar matakin da ya kamata kasancewar yawancinsu matan sun yi ikirarin cewa an gayyace su zuwa daurin auren ne daga jihohin da ke makwabtaka.
“Za mu tabbatar da ganin cewa an kama Abba da Mujahid.”
Ibrahim ya jaddada cewar hukumar ta jajirce don kawar da duk wasu munanan dabi’u a jihar.
Aminiya ta rahoto cewa babban kwamandan hukumar, Sheikh Haruna Ibn Sina ya ce wasu daga cikin wadanda aka cafken sun nemi a sassauta masu bisa sharadin ba za su sake aikata laifin ba.
Amarya ta fasa auren angonta ana gab da daura masu aure
A wani labarin kuma, wata amarya ta hau sama ta ce bata auren angonta a lokacin da ake gab da daura masu aure a coci.
Fasto ya lura da yadda amaryar ta shiga tsaka mai wuya, hakan yasa ya tambayeta ko ta shirya ma auren amma ga mamakin mutane sai ta amsa da a'a.
Asali: Legit.ng