An Fara: Yadda Wani Amfani Da POS Yai Kuka Wiwi Sabida Yadda Aka Bashi Jabun Kudi

An Fara: Yadda Wani Amfani Da POS Yai Kuka Wiwi Sabida Yadda Aka Bashi Jabun Kudi

  • A wani faifen bidiyo da ya yadu, ya nuna yadda aka damfari wani amfani da POS da 'yan N1000 na jabu
  • A cikin Bidiyon anga yadda mutumin ke korafi kan yadda aka bawa matarsa kudin jabu kuma 'yan N1000
  • Bankuna kasuwanci a Nigeria sun fara raba sabbin kudi a ranar alhamis din nan da ta gabata.

Kwanaki kadan bayan da babban bankin kasa ya saki sabbin kudaden da ya canjawa fasali wanda suka hada 'yan N1000, N500 da kuma N500, an fara samun yaduwar jabunsu a hannun al'umma.

Bidiyon wani mai yin sana'ar hada-hadar wakilin banki wanda ya shafi cirar kudi, bude akawun da sanya kudi a ciki ya bayyana inda ya nuna yadda aka bashi jabbun kudin.

A cewarsa

"Sabbin kudin suna da wani tambari mai ruwan gwal a jiki wanda in an karta baya gogewa. Shi kuwa tsohon kudin da wanda aka damfaresun da shi bashi da irin wannan shedar."

Kara karanta wannan

Ana Fargabar Jabun Kudi Sun Fara Yawo A Tsakanin Al'umma Sai Ayi Hattara

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A bidiyon da ke sama mutumin na cewa

"Jama'a ayi hattara, jabun kudi ya shigo kasuwa, dole ne mu hankalta kuma mu lura sosai, dubi yadda tsohon kudin yake, kalli yadda na jabun yake, kamar yadda kuke gani. "

Ba wanda ya isa ya kirkiri Jabun wannan kudaden

Legit.ng ta rawaito cewa tunda fari babba daraktan kula da hada-hadar kudi na da gudanarwa na bankin Ahmed Bello Umar yace 'yan Nigeria su kwantar da hanakalinsu, yana mai rantse musu ba wanda ya isa ya kirki na jabu.

Yana Mai Cewa:

"mun shirya sosai wajen ganin mun inganta wannan sha'anin kudin na CBN kuma mun tabbatar mun aiki dan gudun kirkirar wanda yake na jabu ne"

Sabbin Kudi Sunyi Karanci

Sai dai a wani rahoto na musamman da Legit,ng ta fitar ya nuna yadda sabbin kudin sukai karanci a hannun mutane, musamman ma in kaje banki karba ko cirarsu.

Kara karanta wannan

Wata Mata Tace Allah-Fa-Fir Bazata Karbi Sabon Kudi Ba, Sabida Jabu Ne

Kudin
An Fara: Yadda Wani Amfani Da POS Yai Kuka Wiwi Sabida Yadda Aka Bashi Jabun Kudi Hoto: Presidency
Asali: UGC

Babban Bankin Kasa yace duk wanda ya wulakanta kudin kasar nan birsin zai tafi.

Babban Bankin CBN, ya yi gargadi ga 'yan Nigeria bkan su maida hankalinsu wajen gudu ko kin wulakanta kudin kasarnan.

Yana mai tabbatarwa da 'yan kasar duk wanda aka samu da wannan laifin zai fuskanci fushin kuliya.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida