Shugaban Kamfanin Twitter Na Shirin Yin Murabus Daga Matsayin CEO

Shugaban Kamfanin Twitter Na Shirin Yin Murabus Daga Matsayin CEO

  • A watan Oktoban wannan shekarar mai kamfanin Twitter ya sai da kamfanin ga Elon Musk
  • Twitter na cikin manyan kafafen sadarwar zamani da a yanzu al'ummar duniya ke amfani da ita wajen isar da sako.
  • A Nigeria gwamnati ta dakatar da shafin, sabida janye maganganun shugaba Buhari, sai da aka samu masalaha tsakanin gwamnati da kamfanin sannan aka bude ta

Amurka: Sabon shugaban kamfanin Twitter, Elon Musk, ya ce yana ganin zai iya ajiye aikin shugabancin kamfanin, bayan shafe wata biyu da zaman akan muƙamin.

Elon ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter inda yace a kada kuri'ar goyan bayan ya ci gaba da kasancewa a kan kujerar ko a'a, kuma yace zai amfani da abinda kuri'a ta nuna.

A safiyar yau Litinin, awa shida kan a rufe zaben, sakamakon ya nuna ya sauka ya samu kashi 56.3%, kar ya sauka kuma 43.7%

Kara karanta wannan

Wata Mata Ta Tsinke Mijinta Da Mari Ana Tsaka Da Bikin Aurensu, Shima Ya Rama

Tun bayan da ya sai kamfanin kuma ya zama shugabansa a watan Oktoba, sabon shugaban ya fito da shedar tabbacin sahihancin shafi da wasu kaloli maimakon ruwan shuɗi kawai.

Bayan da ya sai kamfanin ya fitar da wasu sabin dokoki da ka'idoji wanda yake ganin sun fi ye masa. Wanda ya hada da sauke wasu masu múkami da daraktocin kamfanin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Elon Musk
Shugaban Kamfanin Twitter Na Shirin Yin Murabus Daga Matsayin CEO Hoto: CBNC
Asali: UGC

Elon ya kori duk wanda yaga bazai iya bin ƙa'idojin da ya gindaya ba. Sannan yace sahihancin shafi da ake sawa mutane yanzu ya zama na kudi in kana da shi zaka ringa biyan wasu kudade, yayin da kuma in kana so zaka siya.

Elon ya dakatar da wani zaure da ake tattaunawa a dandalin Twitter (Twitter Space) din sakamakon wata muhawara mai zafi da sukai da mai Kula da zauren.

Kara karanta wannan

Daliban Abdul-Jabbar Sun Magantu Kan Hukuncin Da Kotu Ta Yanke, Sunce Akwai Lam'a

Yanzu dai abin jira a gani shine ko shi Elon din zai sauka daga mukaminsa bayan kammala zaben ko kuwa.

Wata Biyu Kenan: Amma Har Elon Na Ƙokarin Sauka Daga CEO Din Twitter

Mai kamafanin Twitter Elon Musk ya bayyana a shafin sa jin ta bakin mutane kan ya sauka daga mukaminsa ko kuwa ya ci gaba da zama a matsayin shugaban kamfanin

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida