Tun Bayan Samun Nasara A Zabe Buhari Yayi Watsi Da Mu, Kungiyar Miyetti Allah
- Kungiyar Miyetti Allah ta tuhumci Shugaba Buhari da watsi da Fulani Makiyaya tun da ya lashe zabensa a 2019
- Sabon Shugaban kungiyar Baba Ngelzarma ya zanna da manema labarai don bayyana bacin ransu
- Kungiyar na daga cikin wadanda suka yi tsayin daka don ganin Shugaba Buhari ya yi nasar a 2019
FCT, Abuja - Shugaba kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN), Baba Ngelzarma, ya tuhumci Shugaba Muhammadu Buhari da watsi da makiyaya duk da goyon bayan da suka yi masa a zaben 2019.
Ngelzarma, wanda ya rike kujerar sakataren kungiyar a baya ya samu nasara a zaben da akayi ranar Asabar, 17 ga Disamba, 2022.
Sabbin wadanda aka zaba matsayin shugabannin kungiyar sun hada da Sakatare na kasa, Bello Aliyu Gotoma; da Sakataren kudi, Idris Bawa.
Bayan nasararsa, ya zanna da manema labarai a birnin tarayya Abuja.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yace:
"Yayinda ake gab da zaben wa'adi an biyu na Buhari, mun mara masa baya. Mun nunawa duniya cewa muna tare da shi, amma har ila yau babu abinda ya tsinana mana."
"Buhari ya yi watsi da makiyaya. Gwamnatin nan ta yi banza da makiyaya. Cikin shekaru takwas da suka shude, an kashewa manoma sama da N500bn amma makiyaya ko sisi."
Ya ce duk da tsarin kawo sauyin sashen kiwo da gwamnatin Buhari tayi, babu amfanin da wannan tsari zai yi wajen magance matsalolin makiyaya.
Dalilin da yasa garkuwa da mutane ya zama kaya a wuyar al'umma, Ngelzarma
Ngelzarma ya yi tsokaci kan lamarin Fulani yan bindiga masu garkuwa da mutane da kuma yadda suka addabi al'umma.
Ya bayyana cewa rikon sakainar kashin da gwamnati ta yi wa rikicin manoma da makiyaya ne ya haddasa matsalar.
A cewarsa:
"Abinda muka fuskanta kafin yanzu, a 2013 da 2014, shine rikicin manoma da makiyaya, amma saboda ba'a kula da abin yadda ya kamata ba, ya rikida ya zama satar shanu kuma wani dan ta'adda a jihar Benue mai suna 'Gana' ya fara."
"Yayinda matasan suka rika, sai suka koma garkuwa da mutane saboda an fi samun kudi cikin gaggawa. Yayinda ake cigaba da satar shanu, ana garkuwa da mutane."
Shi yasa idan aka kama masu garkuwa da mutane, kimanin biyar cikinsu Fulani ne. Basu da wata mafitane saboda babu ilimi, babu kasuwanci. Sabosa haka idan aka cigaba da sace musu Shanu, zasu cigaba da tada hankalin jama'a
Asali: Legit.ng