Yanzu Yanzu: Bata Gari Sun Sake Kona Wata Kotu a Jahar Imo

Yanzu Yanzu: Bata Gari Sun Sake Kona Wata Kotu a Jahar Imo

  • Wasu yan daba sun banka wuta a kotun majistare na Owerri, babban birnin jihar Imo
  • Lamarin wanda ya afku a ranar Lahadi, 18 ga watan Disamba, ya yi sanadiyar konewar kayan kotu masu muhimmanci da wasu takardu
  • Rundunar yan sandan jihar Imo ta ce ta kaddamar da bincike don gurfanar da masu laifin

Imo - Wasu mutane da ake zaton bata gari ne sun kona wani sashi na kotun Majistare da ke Owerri a jihar Imo.

Hakan na zuwa ne kimanin sa'o'i 24 bayan wasu yan daba sun kona babban kotun Orlu.

Jihar Imo
Yanzu Yanzu: Bata Gari Sun Sake Kona Wata Kotu a Jahar Imo Hoto: Punch
Asali: UGC

Kotun majistaren wanda ke a tsakiyar babban birnin jihar a nan ne babban kotun Owerri yake.

Jaridar Punch ta rahoto wata majiya na cewa wadanda ake zargin sun zo da abubuwan fashewa sannan suka hari wani sashi na rufin ginin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Darikar Tijjaniya A Nigeria Sun Marawa Bola Ahmed Tinubu Baya

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yayin da ba a tabbatar da irin barnar da harin ya yi ba, an tattaro cewa muhimman kayan kotu da takardu sun kone.

Majiyar ta ce:

"Yan bata gari sun kona wani bangare na kotun majistare da ke hanyar Owerri-Orlu. Abun ya faru a yau (Lahadi). Wannan abun takaici ne."

Da ta ziyarci wajen da yammacin rabar Lahadi, jaridar Punch ta lura cewa hayaki na fotowa daga bangaren ginin kotun da aka kona.

Rundunar yan sanda ta yi martani

Da aka tuntube shi, kakakin yan sandan jihar, Micheal Abattam, ya tabbatar da faruwar labarin sannan ya bayyana cewa an kashe wutan.

Ya kuma sanar da cewar rundunar ta fara gudanar da bincike da nufin kama wadanda suka aikata ta'asar, rahoton Vanguard.

Yan daba sun bankawa babban kotu wuta a jihar Imo

A wani lamari makamancin wannan, bata garu sun bankawa ginin babban kotun jihar Imo wuta a ranar Asabar, 17 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

An Bankado Yadda Ake Tilasta Wa Mata Siyar da Katunan Zabensu Kan N2000 a Arewacin Najeriya

Maharan sun kona muhimman kaya da takardu a harin.

Lamarin ya kuma faru ne yan kwanaki bayan wasu yan bindiga sun farmaki hedkwatar hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta da ke Owerri, wanda ya sanda suka ce yan IPOB ne da aika-aikar.

An kuma tattaro cewa ginin da aka farmaka na dauke da babban kotu da kotun majistare a tare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng