Abduljabbar: MURIC ta Magantu Kan Hukuncin Kisa ta Hanyar Rataya
- Kungiyar kare hakkin musulmai ta jinjinawa babbar kotun shari'a ta Kano bisa yankewa malamin addinin musuluncin nan, Abduljabbar Kabar, hukuncin kisa
- Hakan ya biyo bayan kama shi dumu-dumu da laifin batanci ga fiyayyen halitta a wa'azozinsa da furuci a al'ummar musulmai da ya dade yana yi
- Shugaban MURIC din yayi kira ga musulmai da su kasance masu hakuri da barin shari'a ta dauki mataki a duk lokacin da lamari mai kama da haka ya auku
Kungiyar kare hakkin musulmai (MURIC) ta jinjinawa babbar kotun shari'a ta Kano kan yankewa malamin addinin musuluncin nan hukuncin kisa bayan kama shi dumu-dumu da laifin batanci ga Annabi Muhammad ( SAW).
Yayin yanke hukuncin a ranar Alhamis, Ibrahim Sarki Yola, alkali mai shari'a ya yankewa Abduljabbar Nasiru Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa furucin batanci ga Annabi Muhammad (SAW).
Jaridar TheCable ta rahoto cewa, Muhammad Aliyu, shugaban MURIC, a wata takarda da ya fitar ranar Asabar, ya ce matsayin batanci a shari'ar ya tabbata a kotun koli.
"MURIC ta jihar Sokoto tayi jinjina ga babbar kotun shari'a ta Kano da ta yankewa Abduljabbar Nasiru Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa furucin da dama da yayi na batanci ga fiyayyen halitta.”
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
- Kamar yadda takardar ta karanta.
"Wajibi ne a san cewa hukuncin da umarnin da kotun tayi bayan yanke masa hukuncin kisa shine umartar gwamnatin jihar Kano da ta kwace masallatansa biyu da umartar duk kafafan sada zumuntar zamani da su kiyayi amfani da wa'azozi da hotunansa.
"Dokar shari'a ce sananniya karkashin shari'ar musulunci hukuncin kisa ga duk wanda yayi batanci ko suka ko cin zarafi ga Annabi Muhammad (SAW).
"Wannan matakan shari'ar kotun koli ce ta tabbatar dashi a shari'a ta shekarar 2008 mai lamba 7 NWLR (Pt. 1085) 125, ratio 15, in ta ce: A shari'ance , duk wani mutum mai hankali, kuma baligi musulmi da yayi batanci, cin zarafi ko furta kalamai ko wani mataki da ka iya jawo rikici, zubda jinanai ko taba jalabin Annabi mai daraja Muhammad (SAW). wannan mutumin ya aikata laifi da hukuncin shi kisa ne.
"Haka zalika, Mutanen Kano sun cancanci a jinjinawa musu bisa kin daukar doka a hannunsu a lokacin da lamarin ya auku. Sai dai, sun bar gwamnatin Kano ta dauki matakin kamar yadda addinin Islama ya koyar.
"Daga karshe, muna rokon musulmai da su kasance a koda yaushe masu barin shari'a ta dauku mataki a duk lokacin da mata matsala irin wannan ta auku ba tare da daukar doka a hannunsu ba. Allah ya karawa Annabi Muhammad (SAW) daraja.”
- Takardar ta kara da cewa.
Asali: Legit.ng