Yadda Wata Yar Kasuwa Ta Tubure Taki Karbar Sabbin Kudin Da CBN, Suka Shigo DA Shi

Yadda Wata Yar Kasuwa Ta Tubure Taki Karbar Sabbin Kudin Da CBN, Suka Shigo DA Shi

  • Da yiwuwan jami'an gwamnatin tarayya basu yi isasshen aiki wajen wayar da kan mutane kan sabon kudi ba
  • Wata yar kasuwa taki Amincewa da karbar sabbin takardun kudi da wani abokin cinikaiyyata yayi kokarin bata
  • Matar tace ita bata waye da wannan kudin ba dan haka ya canja mata da wanda ta saba dashi

Wata yar kasuwa ta ki karbar takardar kudin Naira da aka sake fasalin sabida tana zargin bana gaske bane

A cikin wannan bidiyon, 'yar kasuwa, wacce ke gudanar da kasuwanci ta ce ba za ta karbi kudin daga abokin cinikinta ba.

Abokin ciniki ya tambaya,

"Ba ka taɓa ganin wannan ba?" sai ta amsa da "A'a ni ban taba gani ba."

Mai siyan abun a wajenta ya birkice yana tambayar wadda zai siya a wajenta

Kara karanta wannan

Ta bare: Saura kiris biki ango ya gano budurwarsa na da 'ya'ya 2, ya dauki tsattsauran mataki

"baki taba gani ba fa kika ce"

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga baya ya dauko tsohon kudi ya bata sannan matar ta amana da siyaryar da zaiyi.

kalli bidiyon a kasa:

Wani Sai Da Kayan Marmari Yaki Karbar Sabbin Kudi

A wani labarin mai kama da wannan, Legit.ng Hausa ta rawaito wani rahoto da wata mata da ake kira da Mama ta je yin siyayya kuma wanda zata sai abun a wajemsa yaki karbar kudi.

Bidiyon da ya yadu a Tik-Tok, ya nuna yadda matar ke fadawa mutumin ya karbi kudin domin sune sabbin kudin da bankin CBN, ya shigo da su.

Amma mutumin yace shi bai sansu ba, abinda ya sani tsoffin kudi. Haka kuma akai matar ta dau kudin ta bashi ko ta biyashi da tsoffin.

Kara karanta wannan

Mai Sayar da Kayan Marmari Yaki Karban Sabon Kudin Da CBN Ya Fito Dashi, Yace Jabu Ne

Shin Akwai Kalubale dan Gane da Sabbin Kudin Da Bankin Ya Shigo da Shi

Kudade da aka canja ba gaba daya bane, iya wasu ne wanda bankin ya nuna su yayin da ake kaddamar da canjin.

wanda aka canja din sun hada 'yan N200 da kuma 'yan N500 sai kuma uwa uba 'yan N100.

Sune dai kudade da CBN, ya Kaddamar a ranar 15 ga watan Nuwanban shekarar 2022 a fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da wasu jiga-jigan gwamnati. Kamar Yadda BBC Hausa ta rawaito

Kalubalen dai bazai rasa nasaba da sabonsu a tsakanin yan kasuwa da kuma dai-daikun al'umma ba. Akwai bukatar daukar dan lokaci kafin kowa ya saba da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida